Kotu a jihar Rivers ta yanke wa Emmanuel Thompson hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekara 22 bayan an kama shi da laifin yi wa ‘yar cikinsa fyade.
Alkalin kotun Eyo Ita ta yanke hukuncin haka ne ba tare da ta bai wa Thompson damar ya nemi beli ba.
Eyo ta ce ta yanke wa Thompson wannan hukunci ne bisa ga hujjojin da aka gabatar a kotu da suka tabbatar cewa lalle ya aikata wannan abin kunya.
Rundunar ‘yan sandan jihar sun Kama Thompson ne bayan mahaifiyar yarinyar ta kai kara a kungiyar ‘Basic Rights Counsel Initiative’ kan yadda mijinta kuma mahaifiyar yarinyar ya maida ta tamkar matarsa.
Kungiyar ta gabatar da hujjoji Wanda suka tabbatar a kotun cewa Thompson ya dade yana lalata da ‘yar cikinsa mai shekara 14.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga yadda wata kotun sauraren kararraki dake Ore jihar Ondo ta daure wani mahaifi mai suna Moses Peter a kurukuku har sai ta kammala bincike da tattaunawa da fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na ma’aikatar jindadi da walwalar jama’a.
Alkalin kotun F. O. Omofolarin ya yanke hukuncin haka ne bayan shaidu da hujjoji sun tabbata cewa wannan mutum mai suna m Peter ya rika yin lalata da ‘yar cikinsa Patience dake da shekaru 17 kuma a dalilin haka har ciki ya shiga.
Peter ya rika danne ‘yarsa Patience tun daga watan Nuwanba 2020 zuwa Janairu 2021 a cikin gidan sa dake Asewele Korede.
Peter ya amsa laifin da ya aikata sannan ya roki sassauci daga kotu.
Lauyan da ya shigar da karan Amuda ya roki kotu ta dage shari’ar har sai ta kammala yin shawara da fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka.
Kotu za ta ci gaba da shari’a ranar 21 ga Fabrairu 2021
Discussion about this post