BINCIKE: Kashi 80% na manoman Najeriya sun fuskanci ambaliya da fari a 2020

0

Kusan kashi 79% na manoma a Najeriya sun fuskanci matsalar ambaliyar ruwa ko kuma ta fari a cikin shekarar da ta gabata ta 2020.

Wani bincike da aka gudanar a cikin jihohi bakwai na kasar nan ne ya nuna haka.

Cibiyar bincike ta SBM Intel ce ta bayyana haka cewa amfanin gonar kashi 26.3% ya samu tawaya sosai a cikin kakar wacca shekarar ga manoman Najeriya.

Baya ga ambaliya, sun kuma bayyana matsalar fari ko karancin ruwan sama a wasu wurare

Binciken mai take: “Abinci Kawai ‘Yan Najeriya Ke Bukata”, an buga shi cikin wannan wata inda aka zayyana manyan kalubalen da su ka dabaibaye manoman Najeriya da kuma harkar safarar kayan amfanin gona na abinci.

Binciken ya nuna tsoron cewa matsallar da amballiyar ruwa da kuma fari suka haifar ga harkokin noma a cikin 2020, za ta iya shafar shirin bunkasa kasa da abinci.

An kaddamar da binciken a jihohin Nasarawa, Osun, Benue, Oyo, Katsina Ogun da kuma Lagos.

PREMIUM TIMES ta buga rahoton da SBM Intel ya buga a ranar Talata ya maida hankali ne wajen gudanar da binciken kwakwaf a kan lamarin, ta yadda za a bi hanyoyi daban-daban wajen magance wadannan manyan matsaloli.

Rahoton ya maida hankali ne wajen samun bayanai daga manoma da kuma masu safarar kayan abinci daga garuruwa daban-daban a jihohi bakwai da su ka hada da Lagos, Ogun, Oyo, Nasarawa, Osun, Katsina da kuma Benue.

Har yau rahoton ya nuna damuwa a kan yadda wasu kayan gona ke saurin lalacewa saboda babu hanyoyin adana su zuwa wani tsawon lokaci. Wato tilas za a sayar da su a lokacin da aka debe su daga gonaki ko lambuna ko wasu kasuwanni.

Binciken da SBM Intel ya yi ya nuna kusan kashi 47 bisa 100 na manoman da aka ji ta bakin su, ba su da hanya ko wadatar dabarar adana kayan gona masu saurin lalacewa.

Wasu kashi 5.33 na manoma da masu safarar kayan kuma sun bayyana cewa matsalar rashin kyan hanya ne babbar matsalar da ta fi damun su wajen safarar kayan abinci.

Kashi 25 bisa 100 sun ce akwai matsallar yawan haraji barkatai ko a kan titi ko a kasuwanni.

Sai kuma kashi 21.7 su ka ce abin da ke damun su shi ne akwai yawan gallazawar da jami’an tsaro ke yi masu ta hanyar tare su su na karbar kudade a hannu su.

Sun ce rahin kyawon hanyoyi na kawo cikas ta hanyoyi da yawa ga kayan abinci.

Yayin da ake kaurace wa wasu garuruwan saboda matsalar rashin kyan hanya, sau da yawa kuma motocin daukar kayan abinci kan bugi ramu su fadi, kayan abincin su lalace a kan hanya.

A kan haka ne SBM Intel ke ganin cewa samun tsarin safarar kayan abinci ta hanyar zirga-zirgar sufurin jiragen kasa zai rage wannan matsala matuka, kuma za ta rage hauhawar farashin kayan abinci.

“Samun kyakkyawan tsaro abu ne muhimmin kwarai, sai kuma samun hanyar shiga wuraren dauko kayan abinci masu kyau tare kuma da tsarin noman rani mai inganci.”

Sauran ababen da ake bukata sun hada da kudade da wurin adana kayan abinci da sauran su.

“Masu safarar kayan abinci na bukatar samun hanyoyin noma masu kyau da kuma rage masu dan karen haraji daban-daban da ake tatsa a kullum a hannun su. Sai kuma matsalar yadda jami’an tsaro ke takura masu su ka karbar kudade a hannun su.”

Yawancin mnoman da aka ji tabakin su dai manoman kayanabinci ne sai kuma masu noma kayan marmari da kayan miya da rogo da masara.

An samu ambaliya a Bauchi, Kebbi, Neja, Sokoto, Zamfara da wasu sassan jihar Kwara.

“A jihar Kebbi kadai ambaliya ta lalata hekta 500,000 ta amfanin gonar da ya kai naira bilyan biyar.”

Share.

game da Author