Hukumar Kula Da Rikita-rikatar Basussuka ta Najeriya (AMCON), ta bayyana cewa mutum 350 masu taurin bashi ne Najeriya ke bi naira tiriliyan 3.6.
Wadannan adadin mutane su ke rike da naira tiriliyan, su ke rike da kashi 80 bisa 100 na adadin bashin naira tiriliyan 4.4 da AMCON ta ce ta ke bashi.
Shugaban Bangaren Tilasta Biyan Bashi da Kwace Kadarorin Masu Taurin Bashi, Joshua Ikioda ne ya bayyana haka a wani taron sanin makamar aiki da hukumar ta shirya wa jami’an kula da sharkokin shari’a na Babbar Kotun Tarayya na fadin kasar nan.
An bude taron a Abuja, inda Ikioda ya yi bayani kan matsalar da masu taurin bashi su ka haifar wa tattalin arzikin Najeriya.
“Da za a iya karbo wadannan kudade da ke hannun mutum 350, har naira tiriliyan 3.6, to sun isa a farfado da masana’antar sarrafa karafa ta Ajaokuta da ke jihar Kogi.
“Sannan kuma duk a cikin kudin za a iya karfafa wa mutum 200,000 masu kananan sana’o’i da jarin naira milyan 2 kowanen su.”
Ya kara da cewa idan aka yi hakan, an kara samun aikin yi ga dimbin matasa kuma tattalin arziki zai bunkasa a kasar nan.
Daga nan sai ya yi kira ga sauran hukumomin da ke da alaka da bibiyar kadin kudade su taimaka wa AMCON ta kwato wadannan makudaan kudade ga masu taurin bashi.
“Adadin bashin nan na naira tiriliyan da aka rike wa Najeriya, sun fa zarce naira tiriliyan 3.85 na kudaden da Najeriya za ta kashe wajen gudanar da manyan ayyuka a cikin kasafin kudade na 2021.” Inji shi.
“Sannan kuma wadannan kudade sun zarce naira tiriliyan 3.12 wadanda Najeriya za ta biya a matsayin rage bashin da ake bin ta daga kasashen waje a cikin shekarar 2021.
“Kuma wadannan kudade sun zarta kudaden albashin da gwamnati za ta biya ma’aikata na naira tiriliyan 3.7 a cikin shekarar 2021.”
Aikin Hukumar AMCON:
An kirkiro Hukumar AMCON a cikin 2010 domin bin kadin kudaden da bankuna su ka bayar, amma ba a biya ba.
Gudun kada bankuna su karye sakamakon basussukan da su ka bayar, gwamnati kan tari aradu ta hanyar sayen bashin da bankuna ke bi. Ita kuma gwamnati sai ta kwace kadarorin da mai karbar bashin ya bayar a matsayin ‘garanto.’
Aikin hukumar shi ne ta kwato wadannan basussuka ta maida su ga gwamnati, domin bunkasa tattalin arzikin kasa.
A cikin shekaru goma bayan kafa hukumar, AMCON dai ta kwato naira tiriliyan 1 kacal daga hannun manyan masu taurin bashi.
Ta karbo kudaden ne ta hanyar kwace kadarorin su, fawwala wa gwamnati kadara daga mai taurin bashin da ya kasa biya, sai kuma karbar kudade daga hannun wasu da aka taka ruwan cikin su, har su ka amayar da kudaden.