JIRAN GAWON SHANU: Babu ranar fara aikin titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano, saboda rashin kudi –Amaechi

0

“Idan fa ba mu samu wannan bashin na dala bilyan 5.3 daga Chana ba, to ba za mu iya fara aikin titin jirgin kasa din zuwa Kano ba.”

Shekara daya bayan bada kwangilar aikin titin jirgin Kasa daga Ibadan zuwa Kano, yanzu kuma za a iya cewa an yanka ta tashi. Domin Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewa babu alamar kudin da za a fara aikin tukunna.

Amaechi ya ce har yau babu ranar fara aikin, saboda har yau gwamnati na jiran tsammanin amincewar Chana ta yarda za ta bada kudaden da za a yi aikin tukunna.

Amaechi ya ce har yau ana zaman jiran tsammanin amincewa daga Chana ta ce ta amince za ta bai wa Najeriya ramcen kudaden tukunna.

Ya ce kudaden da ake jiran a amince za a bayar su ne dala bilyan 5.3 kafin a fara aikin.

“Gwamnatin tarayya za ta fara aikin titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano, da zaran Chana ta bayyana amincewar ta za ta bayar da kudaden naira bilyan 5.3.”

Gwamnatin Najeriya dai ta dogara ne kacokan a kan bashi daga gwamnatin Chana, domin aikin titin jirgin daga Ibadan zuwa Kaduna.

Tuni dai an kammala aikin titin jirgin daga Lagos zuwa Ibadan.

Murna Ta Koma Ciki:

Minista Amaechi ya bayyana cewa akwai wasu masu zuba jarin a farko su ka amince za su zuba kudaden su. Amma kuma kamar yadda ya bayyana wa gidan talbijin na NTA Abuja, sai masu zuba jarin su ka noke.

Ya ce ita dai gwamnatin tarayya ta rigaya ta amince da kwangilar.

“Abin da kawai aka yi a shekarar da ta gabata shi ne amincewa da kwangilar aikin.”

“Mutane sun dauka tun daga ranar da na bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bada kwangillar aikin titin jirgin kasa ga kamfanin CCECC, daga Ibadan zuwa Kano, sun dauka akwai kudin da za a fara aikin kenan. To abin ba haka ba ne.

“Har yau ba mu da ko sisin da za mu fara wannan aiki, bayan shekara daya da mu ka rubuta takardar neman bashin kudin da za a yi aikin tititin na jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano.

“Idan fa ba mu samu wannan bashin na dala bilyan 5.3 daga Chana ba, to ba za mu iya fara aikin titin jirgin kasa din zuwa Kano ba.” Inji Amaechi.

Share.

game da Author