Sakamakon gwajin cutar korona da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta CDC ta fitar ranar Lahadi ya nuna cewa mutum sama da miliyan 3 sun kamu da cutar korona a Afrika. Tun bayan bullowar cutar a Afrika kimanin watanni 11 da suka gabata sannan cutar ta kashe mutum 72,000.
Kasashen Afrika ta Kudu, Morocco, Masar, Tunisia, Ethiopia, Libya, Kenya, Algeria da Najeriya ne kasashen da cutar ta fi yaduwa a cikin su.
A lokacin da cutar ta fara bullowa a Nahiyar Afrika gwamnatocin kasashen Afrika sun saka dokar hana shiga da fita kasashen su tare da saka dokokin kiyaye kamuwa da cutar.
Sai dai a wannan karo da cutar ke sake darkakowa a karo na biyu gwamnatocin kasashen Afrika sun sassauta dokar hana shiga da fita kasashen su saboda koma bayan tattalin arziki da kasashen ke fama da su.
Rahotan ‘Reuters’ ya nuna cewa Nahiyar Afrika ta samu karin mutum 500,000 da suka kamu da cutar a cikin wata daya.
A ranar Lahadi adadin yawan mutanen dake dauke da korona a duniya sun kai miliyan 91 sannan mutum sama da miliyan 1.9 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
Cutar ta ci gaba da yaduwa yayin da wasu kasashen duniya ke yi wa mutanen su allurar rigakafin cutar
Zuwa yanzu mutum 3,021,769 ne suka kamu a Afrika inda daga ciki 2,450,492 sun warke sannan 72, 121 sun mutu a Afrika.
Afrika ta Kudu ƙasa ce da cutar ta fi yi wa katutu inda a kasan mutum miliyan 1.2 sun kamu sannan 33,000 sun mutu.
Najeriya itace ƙasa ta 9 a cikin jerin kasashen da cutar ta fi yi wa katutu a Afrika.
Zuwa yanzu mutum 95,934 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 77,982 sun warke, 1,330 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 16,622 ke dauke da cutar a Najeriya.