GOBARA: An yi asarar dukiya da ya kai naira biliyan 2.5, a shekarar 2020 a Kaduna

0

Shugaban hukumar kashe gobara na jihar Kaduna Paul Aboi ya ce gobarar da aka yi sau 615 daga watan Janairu zuwa Disambar 2020 ya yi sanadiyyar rayukan mutum 76 a jihar.

Aboi ya fadi haka ne da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Talata a birnin Kaduna.

Ya ce hukumar ta ceto mutum 85 sannan wasu 135 sun ji rauni.

Aboi ya ce jihar ta yi asaran kaya da ya kai biliyan 2.5 sannan hukumar ta ceto kayan Naira biliyan biyar daga gobaran.

Ya ce an samu karuwan aukuwar godabar daga 523 a shekaran 2019 zuwa 615 a 2020.

Aboi ya ce a mafi yawan lokuta sakacin da mutane ke yi da wutar lantarki ne ke haddasa gobarar.

Ya yi kira ga mutane da su rika kashe kayan dake amfani lantarki a duk lokacin da basa amfani da su.

Bayan haka ya ce hukumar na fama da karancin ma’aikata wanda haka ke yawan sa ma’aikatan hukumar na isa inda gobara ya barke ba da wuri ba da kuma rashin kyawawan hanyoyi.

Aboi ya ce hukumar bada agajin gaggawa na jihar Kaduna za ta hada hannu da hukumar domin wayar wa da mutane kai kan yadda za su rika mutunta ma’aikatan hukumar kashe gobara ta kasa da sauran su.

A makon da ya gabata PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda gobara ta yi sanadiyyar rayukan mutum 134 da dukiyar mutane da ya kai naira miliyan 635 daga watan Janairu zuwa Disambar 2020 a jihar Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce ta ceto rayukan mutum 1,077 da kaya da ya kai na naira biliyan 2.56 a gobara 786 da aka yi a cikin shekarar 2020.

Share.

game da Author