Majalisar zartarwa ta amince da sabon kudiri don kara shekarun ritaya ga malaman Najeriya

0

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da wani sabon kudiri don kara shekarun ritayar malamai a fadin kasar.

Kudirin na neman kara shekarun ritayar malamai daga shekaru 60 zuwa 65 sannan kuma ya kara shekarun da za a yi aiki daga shekaru 35 zuwa 40.

Yanzu haka za a aika da kudirin zuwa majalisar Kasa don domin su yi aiki a akia yadda ya kamata kafin ya zama doka, in ji Ministan ilimi, Adamu Adamu, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja bayan taron FEC.

‘Tsarin Daidaitawar shekarun ritaya ga malamai a Najeriya, 2020’, na neman bada goyon baya ga doka ga sabbin matakan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka don bunkasa aikin koyarwa a kasar.

“Wannan kudiri da aka amince da shi ga Ma’aikatar Ilimi, wani babban mataki ne na abin da muka sa a gaba a shekarar da ta gabata, don haka, a taron da aka yi a yau, Majalisar ta amince da cewa za a aika da kudirin wanda za a kira ‘shekarun da ya dace na ritaya ga malamai a Najeriya 2020’ ga Majalisar Dokoki ta Kasa don sanya su cikin doka ta yadda duk alkawurran da shugaban ya dauka su samu gindin zama a daram dam.”

“Ainihin kudirin a zahiri shi ne bada goyon baya ga doka don amincewa da sabon shekarun ritaya na 65 ga malamai sannan kuma a kara wa’adin aikin malunta zuwa shekaru 40.”

Baya ga kara yawan shekarun ritaya da kuma shekarun yin aiki, kudirin ya kuma nemi a rika ba malamai lambar yabo, alawus na musamman ga malaman dake aiki a karkara da sauran abubuwan da za su karfafa wa hazikan ‘yan Najeriya gwiwar fadawa cikin aikin koyarwa.

“Manufar ita ce don jawo hankalin hazikai ga aikin malunta kuma don haka, shugaban ya amince da sake dawo da kyaututtukan kudade, inganta ingancin malamai, samar da tsarin koyar da dai sauransu. Shugaba Buhari ya kuma amince da cewa ya kamata a samu wasu alawus na musamman, kamar alawus din tura malami zuwa karkara da kuma alawus din malaman kimiyya.”

Share.

game da Author