Mahara sun sako basaraken Adamawa da suka sace – Rundunar ‘Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta sanar cewa mahara sun sako basaraken jihar Ardo Mustapha da suka sace a makon jiya.

Kakakin rundunar Suleiman Nguroje wanda ya tabbatar da haka ranar Laraba ya ce tuni basaraken na gida tare da iyalensa.

A lokacin da aka sace basaraken, Nguroje ya ce jami’an sun fantsama farautar masu garkuwar, don su ceto shi.

“ Lokacin da mu ka ji labarin sace basaraken, Kwamishinan ‘Yan Sanda ya tashi zaratan jami’an kar-ta-kwana domin bazama ceto shi.

“ Ita harkar tsaro ta kunshin kowa, kuma ta na bukatar goyon baya da hadin kan kowa. Don haka a rika ba mu labarin duk wani mutumin da ba a yarda da shi ba, ko wanda ake zargi.”

Nguroje ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin kamo maharan da suka yi garkuwa da basaraken.

Zuwa lokacin da ake rubuta wannan labari babu tabbacin ko an biya kudin fansa kafin aka saki basaraken.

An sace Ardo Mustapha a cikin gidan sa da misalin karfe 12 na tsakar dare a kauyen Mayo-Farang Karamar Hukumar Mayo Belwa.

Share.

game da Author