GOBARAR KASUWAR SOKOTO: Wike ya ba ‘yan kasuwan gudunmawar naira miliyan 500

0

Gwamna jihar Ribas Nyesom ya ba da gudummawar Naira miliyan 500 don tallafa wa Gwamnatin Jihar Sakkwato a sake gina Babbar Kasuwar Sakkwato da gobara ta lalata a safiyar Talata.

Wike wanda ya ziyarci inda lamarin ya afku a kasuwar bayan awanni 24 da afkuwar bala’in, ya nuna damuwa game da wannan ibti’i da ya faru wa ‘yan kasuwan Sokoto.

Mai ba Gwamna Aminu Tambuwal shawara na musamman kan harkokin yada labarai Muhammad Bello, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Laraba.

Gwamnan Wike ya ce wani bangare na gudummawar shi ne don tallafa wa wadanda gobarar ta shafa.

Ya lura cewa duk abin da ya shafi jihar Sokoto ya shafi Ribas, ya kara da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an sake gina kasuwar sannan a tabbatar kasuwa ta dawo kamar da.

Tambuwal ya shaida wa Wike a lokacin da yake zazzagayawa da shi kasuwar cewa kasuwar na da shaguna 16,000 daga ciki akalla kaso 60 cikin 100 gobarar ta shafa.

Bayan duba wurin, Wike da mukarraban sa sun kuma kai ziyarar ban girma ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar a fadarsa.

Ya yi ta’aziyya ga gwamnatin jihar, majalisar masarautar tare da jama’ar ta bisa rasuwar kwamishinan harkokin cikin gida na jihar, Alhaji Abdulkadir Abubakar, kanin Sarkin.

A nasa jawabin, Mai girma sarki Abubakar, ya jinjina dadaddiyar dangantakar da ke tsakanin Sokoto da Ribas, ya nuna godiya ga gwamnan kan ziyarar tasa da kuma goyon bayan da yake ba jihar. Sannan kuma ya yaba wa Tambuwal bisa ayyukan da yake yi a jihar.

Share.

game da Author