Hukumar NDLEA ta kama wasu masu harkalla da safarar muggan kwayoyi a jihar Kano.
Kwamandan hukumar Ibrahim Abdul ya fadi haka a lokacin da yake zantawa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a a garin Kano.
Ya ce hukumar ta kama wadannan mutane a watan Janairu a sassa daban-daban a fadin jihar.
Abdul ya kara da cewa hukumar ta kama tullin muggan kwayoyi da ya kai nauyin kilogiram 581.702.
“Daga cikin wadannan kwayoyi da muka kama akwai hodar ibilis mai nauyin kilogiram 0.097, kwayoyin Psychotropic mai nauyin kilogiram 48.025 da ganyen wiwi mai nauyin kilogiram 553.
Ya ce a tsakanin wannan lokaci babban kotun jihar ta yanke wa mutum hudu daga cikin mutum 43 dake harkallar muggan kwayoyi hukunci.
“Hukumar ta tsare wasu mutane 76 da duk sun samu jikitar kwakwalwa saboda shaye-shaye da miyagun kwayoyi ana kula da su. Amma zuwa yanzu hudu sun warke daga cikin su.
Abdul ya ce hukumar ta samu wannan nasara ne a dalilin maida hankali da jami’an hukumar suka yi na tsananta farautar masu harkallar muggan kwayoyi a fadin jihar. Ya kuma ce ba za su yi kasa-kasa ba wajen ganin an kamo masu wannan sana’a a duk inmda suke.
A karshe ya jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari na nadin da yayi wa tsohon gwamnan jihar Legas, Buba Marya sabon shugaban hukumar NDLEA din.