Masu garkuwa da mutane da masu yin fyade sun Kade a jihar Kebbi

0

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya saka hannu a dokar jihar na 2021 da ya bada damar a yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa sannan da yi wa masu fyade daurin rai-da-rai a jihar.

Antone-janar Kuma kwamishinan shari’ar jihar Ramatu Gulma ta sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Alhamis a Birnin Kebbi.

“Bisa ga tsarin dokar penal code 202 sashi na 247 za a kashe duk wanda aka kama yayi garkuwa da wani kuma sashi na 259 sakin layi na daya a dokar ya ce za a yi wa duk wani da aka kama yayi fyade daurin rai-da-rai.

Ramatu ta ce baya ga wadannan dokoki gwaman ya saka hannu a dokar da zai rage daukar lokaci mai tsawo da kotu ke yi wajen yanke wa masu laifi hukunci a jihar.

Bisa ga tsari dokar ya bai wa alkalai ikon yanke wa wadanda suka aikata kananan laifuka hukuncin da ya kamata a maimakon daure su a kurkuku na tsawon lokaci.

Yin haka zai taimaka wajen rage yawan cinkoson da ake samu a gidajen yarin kasar nan.

Bayan haka gwamnati ta saka hannu a dokar gina kwalejin koyar da ayyukan kiwon lafiya da fasaha a Jega da kwalejin koyar da aikin malunta a Argungu.

Share.

game da Author