Hukumar Ayyukan Gyara da Kula da Titinan Gwamnatin Tarayya (FERMA) ta bayyana cewa gwamnati za ta gyara hanyoyi dake da nisan kilomita 274 a jihar Bauchi.
Shugaban hukumar a jihar Bauchi Nanpan Joroh ya sanar da haka da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a a garin Bauchi.
Joroh ya ce gyaran hanyoyin zai dauki tsawon watanni shida kuma tuni gwamnati ta bada kwangilar gyaran hanyoyin.
“Gwamnati ta bada gyaran hanyar Bauchi zuwa Kari dake da nisan kilomita 137 wa kamfanin ‘JE CON construction Nigeria limited’. Sannan kamfanin ‘AYM Shafa Constructions firm’ zai gyara hanyar Bauchi zuwa Ningi dake da nisan kilomita 97.
Bayan haka Joroh ya ce gwamnati ta sa a fara gyaran hanyar Bauchi zuwa Tafawa-Balewa dake da nisan kilomita 40.
Ya ce gyare-gyaren da za a yi a wannan hanya sun hada cike ramuka, gyara kwalbati da gyara gefen hanya.
A karshe Joroh ya ya roki mutane su rika kai rahoton duk wata hanya da suka ga ta ragwargwabe domin a rika bi ana gyarawa .
Discussion about this post