Hukumar NDE za ta horas da matasa 880 sana’o’in hannu a jihar Kano

0

Hukumar samar da aikin yi NDE ta fara horas da matasa 880 sana’o’in hannu a jihar Kano.

Shugaban hukumar na wucin gadi
Abubakar Nuhu-Fikpo ya ce gwamnati ta yi haka ne domin samar wa matasa da gajiyayyu aikin yi a jihar.

Nuhu-Fikpo ya ce hukumar NDE za ta horas da matasan a karkashin shirin ‘Basic National Open. Apprenticeship Scheme (B-NOAS)’ na tsawon watanni uku.

Ya ce za a bai wa kowani matashi da ake horas jali da kayan aiki ya fara sana’a.

Nuhu-Fikpo ya ce kowacce karamar hukuma a jihar ta aiko da mutum 20 wanda za a horas a karkashin wannan shiri.

Kodinatan NDE ya yi kira ga matasan da za a horas da su mai da hankali su koyi sana’o’in da za a koyar da su domin zama abin amfani wa kansu da al’umma gaba daya.

Share.

game da Author