An fara samun ƙarancin maganin rigakafin Korona a Duniya -Kungiyar WHO

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta koka kan ƙarancin maganin rigakafin Korona da ake fama da shi a duniya.

Wakiliyar WHO dake kasar Rasha Melita Vujnovic, ta sanar haka ranar Laraba a talabijin din ‘Rossiya 24 Channel’.

Metita ta ce karancin maganin rigakafin ya kawo rashin daidaituwa tsakanin kasashen duniya a yanzu haka.

Manyan ƙasashen duniya na ci gaba da warwason maganin don ƴan ƙasashen su, hakan ya sa ruwan magani ya zama gwal sai mai kudi da karfin iko zai mallake shi.

A karshen wannan wata ne gwamnati ta ce za ta karbi maganin Korona da ta yo oda sannan kuma mahukunta sunce da zarar maganin ya iso kasa, shugaba Buhari da mataimakin sa Osinbajo za gabata a talbijin ayi musu rigakafin kowa ya gani domin ƴan Najeriya su amince su yarda suma a yi musu idan aka fara yi gama gari.

A watan Janairu shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya kwabi manyan kasashen duniyan da suka cigaba kan yadda suke warwason maganin rigakafin a kasuwanin ba tare da sun rage wa kasashen masu tasowa ba.

Domin guje wa haka Ghebreyesus ya ce WHO ta sayi kwalaban maganin rigakafin Lorona har biliyan 2, domin agaza wa kananan kasashe masu tasowa.

Zuwa yanzu mutum 96,741,757 suka kamu da cutar korona a duniya. Daga ciki mutum 2, 068, 733 sun mutu sannan mutum 69,431, 809 sun warke.

Share.

game da Author