Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi rantsuwar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai cika alkawarin da ya dauka na mara wa Tinubu baya a zaben 2023 ba.
Lamido ya bayyana haka a taron sasanta ƴaƴan jam’iyyar PDP da aka yi a garin Dutse babban birnin jihar Jigawa.
” Buhari da Tinubu su ne turaku biyu da suka kafa APC, amma ba ri kuji yau daga bakina Wallahi! Wallahi! Wallahi!!!, Buhari ba zai mara wa Tinubu baya a 2023 ba.
” Muhimman abubuwa uku da Buhari ya dauki alkawarin yi wa ƴan Najeriya duk bai cika su ba. Na farko dai ya ce zai samar da tsaro a Kasa, ba a samu haka ba, ya ce zai farfado da tattalin arzikin kasa ba a samu haka ba sannan kuma yace zai yi yaƙi da cin hanci da rashawa duk ba a samu haka ba.
” Yadda tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya yaudari ƴan Amurka, haka Buhari ya ƴaudari ƴan Najeriya shi yasa ƴan Najeriya ke fama da wahalhalu birjik.
” Ina kalubalantar mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya zo ya nuna ƴan jihar Jigawan da gwamnatin Buhari ta fidda daga tsananin talauci ciki miliyan 20 din da gwamnatin ke kurin ta tsamo daga tsananin talauci a Kasar nan”