Gwamnati Tarayya ta dauki mata da matasa 5,000 aiki a jihar Barno

0

A shirin samar da aiki na ‘Extended Special Public Works programme (ESPWs)’ gwamnatin tarayya ta bai wa mata da matasa 5,000 aiki a jihar Barno.

Shirin ESPWs shiri ne da gwamnati ta kirkiro domin farfado da tattalin arzikin ƙasa ta hanyar bai wa mazauna karkara musamman matasa da mata aikin yi.

Shirin ya fara aiki ne a wasu jihohi takwas a fadin kasar nan.

Ganin yadda shirin ya yi nasara a wadannan jihohi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bada umurin a inganta shirin kuma a fadada zuwa sauran jihohin kasar nan.

Karamin ministan harkokin noma Mustapha Shehuri ya sanar da haka ranar Alhamis a garin Maiduguri.

Shehuri ya ce a dalilin wannan shiri kowace karamar hukuma dake karkashin jihar da ake yin wannan shiri za ta mika sunayen mutum 1000 da za a dauka aiki.

” Gwamnati za ta kashe Naira 1.62 wajen biyan albashin wadannan ma’aikata da za a dauka a kowace karamar hukumar kasar nan.

“A yanzu haka kowacce karamar hukumar dake jihar Barno ta kawo mutum 1000 wanda aka dauka aiki karkashin wannan shiri.

Shugaban hukumar samar da aikin yi na kasa NDE Abubakar Nuhu ya bayyana cewa aiyukkan da wadanda aka dauka aimi karkashin wannan shiri za su hada da sharar tituna, kwashe kwata, gyaran magudanar ruwa, yin aikin kwangilolin gina hanyoyin cikin gari da sauran su.

Nuhu ya ce gwamnati za ta wadatar da wadannan ma’aikata da kayan aiki da kayan kariya daga Korona da cututtuka.

Share.

game da Author