Gwamnatin Kaduna ta cafke Almajirai 160 dake gararamba a titunan garin

0

Ma’aikatan duba gari na jihar Kaduna, sun kama yara kanana  har 160 a cikin garin Kaduna da sunan wai su Almajirai.

Gwamnati ta ce ta kama wadannan yara ne a wasu gadaje daidai ku inda ake boyesu wai ana karantar da su.

Cikin yaran da aka kama akwai wasu  ‘yan kasashen Nijar, Burkina Faso da Kamaru.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce gidajen da aka kama wadannan yara basu da lasisin ajiye yara a gidajen, ko kuma wai makaranta.

Gwamnati ta ce doka ne a jibar Kaduna cewa duk yaro a Jihar ya rika zuwa makarantar Boko da gwamnatin jihar ta samar da shi kyauta.

A watan Maris,  gwamnatin Kaduna ta maida Almajirai akalla 31,000 zuwa garuruwansu.

Sannan kuma ita ma jihar an dawo mata da nata almajiran.

Share.

game da Author