Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1867 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –713, Filato-273, FCT-199, Kaduna-117, Oyo-79, Enugu-58 Ondo-53, Kano-49, Sokoto-43, Ogun-37, Osun-37, Nasarawa-36, Rivers-28, Benue-24, Delta-24, Niger-24, Gombe-18,Edo-15, Taraba-12, Bayelsa-10, Ekiti-9, Borno-6, Zamfara-2 da Jigawa-1.
Yanzu mutum 107,345 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 84,535 sun warke, 1,413 sun rasu.
A ranar Alhamis , mutum 1479 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Nasarawa, Rivers, Edo da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Kodinaton Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile yaɗuwar Korona, ta gargadi mutane su daina yaɗa maganganun da ba a yi su ba don tada hankulan mutane musamman game da Korona.
Idan ba a manta ba an rika yaɗa labarai cewa wai gwamnatin tarayya za ta sake garkame kasa saboda darkakowar da Korona ta yi. Saidai Sani Aliyu ya ce wannan magana babu gaskiya a cikin sa.
” Kwamitin shugaban kasa bata taɓa fidda wata sanarwa cewa wai zata sake maida mutane cikin ‘Kulle’ a Najeriya ba. Duk labaran kanzon kurege ne ake yadawa.
Aliyu ya gargadi mutane da su daina yada ire-iren wadannan maganganu da basu da tushe.
” Mu dai a kwamitin mu ba a taɓa kawo wannan magana ba, wasu ne kawai da ke neman kawo ruɗani a tsakanin mutane suke yaɗa karairayi irin haka, su shiga taitayin su tunda wuri, sannan su daina haka.
Makonni biyu kenan a jera ana samun mutane sama da dubu a kullum da suke kamuwa da Korona a kasarnan.
Sai dai hakan bai sa mutane sun shiga taitayin su ba wajen kiyaye dokokin kamuwa da cutar, wato ta hanyar saka takunkumin fuska, wanke hannaye da daina gwamatsuwa ba.