Wata’ yar kunar Bakin wake ta tada bam din dake daure a jikinta a garin Konduga, jihar Barno.
Akalla mutum 3 ne suka mutu a wannan hari.
An ruwaito cewa wannan yar kunar bakin wake ta tada da bam din a kusa da gidan hakimin Konduga.
Wannan matashiyar yarin ta silalo cikin dare ne ta shiga cikin jama’a sannan ta tada da bam fin.
Shugaban’yan bangan garin Konduga, Bello Danbatta ya ce wannan shine karon farko da aka yi irin haka tun bayan watanni 11 da aka kawo harin kunar bakin wake a garin Konduga.
Jihar Barno ta yi fama da hare-haren kunar bakin wake a shekarun baya.
Mutane da yawa syn rasa rayukan su a sanadiyyar irin wannan hari na bazata.