Yayin da sahihin bayanin kididdiga ya tabbatar da cewa Boko Haram sun tare babban titin Damaturu zuwa Maiduguri fiye da sau 60 a cikin shekarar 2020, harin baya-bayan nan da su ka kai a ranar Juma’a sun sun sake arcewa da mutane da dama, bayan sun banka wa wasu motoci wuta.
Cikin motocin da su ka kona har da wata babbar motar daukar manyan kaya ta kamfanin Dangote, wadda kafin su banka mata wuta sai da su ka bindige direban motar.
Akalla an kiyasta sun arce da matafiya za su kai 35 a ranar Juma’a, mako daya daidai bayan sace dalibai 344 da ‘yan bindiga su ka yi a Kankara, Jihar Katsina.
Majiyar da ta ga abin da ya faru ranar Juma’a, ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram sun kai wa matafiya masu dama hari, kuma su ka kona motoci masu yawa.
Wadanda su ka shaida sun ce wannan harin kama matafiya ana shiga daji da su, shi ne na sama da 50 kenan a cikin shekarar 2020.
Keta daji tsakanin Damaturu da Maiduguri mai nisan kilomita 135 abu ne mai hatsarin gaske, musamman ga matafiyan da su ka keta kafin 9 na safe ko kuma bayan karfe 2 na rana.
An tabbatar da cewa akalla akalla sun kona motoci za su kai tara. Wasu ganau a cikin majiyar sojoji, sun tabbatar da cewa “wasu fasinjojin sun ga motoci na cin wuta, amma sai su ka dauka ko daji ne ake Konawa.”
“Amma da su ka kusanci inda wutar ke ci, sai su ka ga Boko Haram sun tunkaro su a kan motoci dauke da bindigogi. Kafin su yi kokarin juyawa baya, har Boko Haram sun cim masu.”
“Da yawan fasinjojin sun tsere a cikin jeji, amma tabbas Boko Haram sun kama 35, su ka kone motoci 9, ciki bakwai na haya ne, biyu kuma ban a haya ba.
Kakakin CJTF Danbatta Bello, ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Ya kuma kara yi wa PREMIUM TIMES karin haske sosai. Ya ce maganar gaskiya wannan hari na baya-bayan nan, an fi dora laifin sa a kan tubabbun Boko Haram, wadanda gwamnati ke yafewa su na komawa cikin jama’a.