Kamfanin sadarwa mai dadin sha’ani da saukin mu’amala ga kwastomomi, wato 9mobile, ya yi hikimar kaddamar da tasha a intanet, wato Yanar Gizo, wadda kwastomomi masu amfani da lambobin waya na 9mobile za su shiga kai-tsaye su hada Lambar Wayar su da Lambar Katin Dan Kasa (NIN).
Wannan tasha da kamfanin ya bude a intanet mai suna www.9mobile.com.ng/nin, tuni ta fara aiki a shafin yanar gizo ta 9mobile, domin samar wa masu amfani da layin wayar kamfanin saukin tantancewa da hada lambobin su da Lambar Katin Dan Kasa (NIN) nan take.
Shiga wannan tasha zai ba masu lambobin 9mobile damar hada lambar su da lambar NIN din su a saukake, ba tare da shan wahalar kokawa da turereniya a Cibiyoyin Tantancewa da aka bude a fadin kasar nan ba.
Wannan mataki da kamfanin 9mobile ya dauka a cikin gaggawa, ya fi kowane mataki saukin tantance lambar NIN tare da hada ta da lambar waya, kamar yadda Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta bayar da umarni.
Wata damar da wannan tsari ya bayar kuma ita ce za a iya amfani da tsarin USSD ta hanyar buga *200*8# a tantance tare da hada lambobin biyu na NIN da na 9mobile.
Jami’in Yada Labarai na 9mobile, Ibikunle Jimo ya ce a matsayin 9mobile na kamfanin da ya san hakkin kwastomin sa tare da gudanar da kyakkyawar hulda da su, kamfanin a ko da yaushe ya na bijiro da hanyoyin saukake aiwatar da lamarin gaggawa, ta hanyar kirkiro hanyoyin da ba sai an sha wahala ba.
“Yayin da muka samu umarnin Hukumar NCC cewa a hada layukan wayaoyi da lambar katin dan kasa (NIN), nan da nan sai muka zaburar da kwararrun jami’an mu na Fasahar Sadarwar Zamani (IT), domin su fito da hanya mafi sauki ga kwastomin mu. Shi ya sa muka bambanta da saura, idan ana maganar hakkin kulawa ga kwastoma ba tare da an bar shi ya sha wahala wajen yin mu’amala da mu ba.
“Wannan kuwa ba sabon abu ba ne a gare mu, dama abin a jinin mu ya ke. Muna kira ga kwastomomin mu da su hanzarta cin moriyar wannan damar ta hanyar tantance lambar katin dan kasa tare da hada ta da layin su na 9mobile a saukake.” Inji Jimo.
Haka nan kuma Jimo ya kara da cewa baya ga wadannan damammaki da kwastomin 9mobile su ka samu, kamfanin ya zuba na’urori a cibiyoyin sa na tantancewa, ga duk wanda ya ke bukatar zuwa cibiyar domin ya tantance.