An bayyana rasuwar mashahurin malami, tsohon Alkalin Alkalai Ahmed Lemu.
Ahmed Lemu shi ne ya taba shugabantar kwamitin binciken hargitsi da kashe-kashen da ya wakana bayan zaben 2011.
Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ne ya nada shi shugabancin kwamitin a lokacin.
Ya rasu ya na da shekaru 91 a duniya. ’Yar sa Maryam Lemu ce ta yi sanarwar mutuwar a shafin ta na Facebook.
“Inna lillahi wa inna liayhi raji’un.
Ina mai cike da bakin cikin rasuwar mahaifin mu Dakta Sheikh Ahmed Lemu OFR, wanda Allah ya karbi ran sa a safiyar yau Alhamis, a Minna.
Za a sanar da lokacin yi masa jana’ida an jima kadan.
“Wassalam, wannan sanarwa ce daga Nuruddeen Lemu, A madadin sauran iyalan mamacin”.
“Ina alfahari da kasancewa ta diyar wadannan mashahuran mutane biyu (wato Lemo da matar sa, wadda Maryam ta buga hoton su a cikin sanarwar rasuwar) Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah.”
Lemo ya yi ritaya ya na mukamin Alkalin Akalai, wato Grand Khadi.
Fitaccen malami ne da ya rubuta littattafai da dama na addinin musulunci.
Ahmed Lemu shi ne ya taba shugabantar kwamitin binciken hargitsi da kashe-kashen da ya wakana bayan zaben 2011.