Majalisar Kolin Harkokin Addinin Musulunci ta yi sabon Mataimakin Shugaba

0

Majalisar Kolin Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) ta yi sabon Mataimakin Shugaba.

Wanda aka nada din, Rasaki Oladejo, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisa na Shiyyar Kudu. Oladejo Mamba ne na Cibiyar Hada-hadar Hannayen Jari.

Wannan sanarwa dai ta fito ne daga bakin Mataimakin Babban Sakataren Majalisar, wadda Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ne shugaban ta.

Cikin wannan makon ne wannan majalisa ta yaba koma ta jinjina wa PREMIUM TIMES dangane da binciken kwakwaf kan kokarin da majaisar ta yi na wanzar da zaman lafiya a kudancin Kaduna.

Daga cikin ayyukan da wannan majalisa ta fi bai wa karfi akwai batun ganin wata, musamman na fara Ramadan, lokacin fara azumi da kuma ranar da za a ajiye.

Wanda aka nada din, Rasaki Oladejo, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisa na Shiyyar Kudu. Oladejo Mamba ne na Cibiyar Hada-hadar Hannayen Jari.

Share.

game da Author