Hamshakin attajiri, Dahiru Mangal, ya ba dan takaran shugaban Kasar Nijar, na jam’iyyar PNDS, Mohammed Bazoum, gudunmawar motocin Kamfen guda 100.
Daya daga cikin jagororin kamfen din Mohammed Bazoum, ya bayyana haka a garin Maradi, a lokacin da manema labarai suka nemi karin bayani game da kyautar.
Mai magana ya ce, wannan kyauta ta fito ne daga hamshakin attajiri, Dahiru Mangal, a matsayin gudunmawar sa ga dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar PNDS, Mohammed Bazoum, wanda shine wanda shugaba mai barin Gado yake goyon baya.
KALLI BIDIYON MOTOCIN DA MANGAL YA BA DAN TAKARA A NIJAR
Jaridar PR Nigeria ne ta ruwaito wannan labari a shafinta, sannan ta saka bidiyon wadannan motoci da Mangal ya bada na gudunmawa.
Dahiru Mangal na daga cikin attajiran Najeriya da suka yi fice wajen harkokin kasuwanci a kasar nan.
Shine kuma mamallakin kamfanin jiragen sama na Max Air wanda aka kafa a 2008.