Shugaba Muhamadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ta ba za ta gajiya ba har sai ta dakile Boko Haram da sauran kashe-kashe da hare-haren da su ka addabi kasar nan.
Buhari yay i wannan jaddadawa a ranar Alhamis a Abuja,
A wurin kaddamar da sabon jirgin yaki daga cikin 23 da ya ce gwamnatin sa ta sayo wa Rundunar Sojojin Sama.
Buhari ya kaddamar da jirgin samfurin Helikwafta NAF MI-171E Da kuma wasu jiragen yaki biyu, Alpha Jets DA KUMA l39ZA.
“A bangaren mu, za mu ci gaba da goya wa hukumar sojojin sama baya ta hantar sayo masu dukkan kaya da makaman da su ke bukata domin tabbatar da tsaron kasa.”
Ya ce gwamnatin sa ta bunkasa kayan fadan sojojin sama, ta hanyar sayo jiragen yaki 23 daga 2015 zuwa yanzu.
“ Wadannan jirage 23 ba su cikin wasu jirage 15 da aka yi odar Super Tucano 12 daga Amurka da kuma wasu 3 daga Pakistan, wadanda ke kan hanyar zuwa.
Shugaban na Najeriya ya ce ya saki helikwafta samfurin Agusta 101 daga jiragen Fadar Shugaban Kasa, ya bada su ga sojojin saman Najeriya, domin kara inganta tsaro.
Buhari ya jinjina wa jami’an tsaro dangane da karin ingancin tsaron da aka samu a Barno, Yobe da Adamawa.
“Don haka ina kara godiya ga ‘yan Najeriya da suka ci gaba da yin amanna cewa za mu iya samar da ingantaccen tsaro ta hanyar kawar da matsalolin ta’addanci da ‘yan bindiga a kasar nan.”
Shugaba Buhari ya ci gaba da bayyana muhimmancin sojojin saman kasar nan, wadanda ya ce an kafa su tun cikin 1964.
Sannan ya bayyana rawar da su ka taka wajen samar da zaman lafiya a kasashe irin su Gambiya, Guinea Conakry, Mozambique, Liberia, Sierra Leone, Mali, Guinea Bissau da Cameroon.