Kungiyar kiwon lafiya ta bude sabon shafi a yanar gizo domin samar wa mutane bayanai game cutar korona da wasu cututtuka.
A wannan shafi da WHO ta bude za a samu kwararrun ma’aikatan lafiya da masu gudanar da bincike guda 13 dake fadin duniya da za su taimaka wajen samar da bayanan cutar.
Kungiyar ta fitar da wannan sanarwa ranar Alhamis din makon da ya gabata.
Gwamnatin Najeriya da UNICEF sun samar da wata layin Kira na waya inda mutane za su iya samun ingantattun bayanai game da korona.
Mutum zai aika da sakon ‘Coronavirus’ zuwa lambar 24453, daga nan za a aiko masa da sakonni game da cutar da matsayin da duniya ke ciki da kasa Najeriya.
Domin shiga wannan dandali a facebook ko Kuma WhatsApp za a iya aikawa da sakon ‘Coronavirus’ zuwa ga +234 908 740 1607. Ko Kuma ta adireshin U-Report kamar haka @ureportnigeria.
Wakilin asusun UNICEF a Najeriya Peter Hawkins ya gargadi mutane da su cigaba da kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar korona cewa yin haka ne kadai mutum zai iya samun kariya daga corona.
Discussion about this post