RASHIN TSARO: Wakilan PDP a Majalisar Tarayya sun buga gangar neman tsige Buhari

0

Wakilan da aka zaba a Majalisar Tarayya a karkashin jam’iyyar PDP, sun yi kira ga al’ummar Najeriya su nemi wakilan su su tsige Shugaba Muhammadu Buhari, saboda ya kasa samar da tsaro a fadin kasar nan.

Sun ce ko ta ina Buhari ya gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, don haka tsige shi ya tafi ya huta kawai shi ne mafita, kuma matakin farko na samun yadda za a wanzar da zaman lafiya a kasar nan.

Wannan furuci na su ya fito ne daga ofishin Shugaban Marasa Rinjaye na wakilan PDP, Kinsley Chinda a cikin wata takardar da ya fitar a ranar Lahadi.

Chinda ya yi bayanin ne sakamakon kisan-kiyashin da aka yi wa manoma 43 a Zabarmari, jihar Barno, ya na mai cewa “Bayanan da su ka fito daga Fadar Shugaban Kasa da kuma bangaren sojojin Najeriya, sun nuna irin yadda shugabanci da jagoranci da gudanar da mulkin gwamnatin Buhari ke tafiyar-k’aguwa da hajijiya da rayukan al’ummar Najeriya ba tare da shugabannin sun damu ba.”

Chinda ya ce ‘yan majalisar tarayya a karkashin PDP na cike da bakin cikin yadda Buhari ya kasa kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, kamar yadda ya yi alkawari.

“Wakilan Majalisar Tarayya da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC na so jama’a daga ko’ina a fadin kasar nan su tilasta wa wakilan su gaggauta tsige Shugaba Muhammadu Buhari, saboda kiri-kiri ya kasa kare ruyuka da dukiyoyin jama’a, kamar yadda ya yi alkawari a karkashin Dokar Tsarin Mulkin Najeriya, Sashe na 14(2)(b).”

Wannan sashe dai ya nuna cewa wasu kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne abu na farko da tilas ake bukata daga kowace gwamnati.

“Yan Majalisar PDP na bukatar Ministoci su kada wa Buhari kararrawar tabbatar da ya gaza tafiyar da shugabanci a Matsayin sa na Shugaban Najeriya mai cikakken iko, kamar yadda Doka ta Sashe na 144(1) ta ce idan ya gaza su buga masa kararrawar tashi daga aiki.”

Sai dai kuma Kakakin Yada Labarai na Majalisar Tarayya, Benjamin Kalu, ya ce ba da yawun Majalisar Tarayya Chindo ya fitar da takardar ba, kawai dai ra’ayin kan sa shi kadai ya fito ya bayyana.

Kalu ya soki yadda Chindo ya fito ya nemi a tsige Buhari, saboda shi Buhari din a matsayin sa na Shugaban Kasa, ya yi wa jama’a bayani, bayan da Majalisar Tarayya ta nemi ya bayyana a gaban ta domin ya yi bayani dangane da munin da matsalar tsaro ke kara yi a fadin kasar nan.

Share.

game da Author