KANKARA 333: ‘Motar Alfa’ ta rubta da ‘yan Najeriya cikin rami – Shugaban CAN

0

A wani kakkausan jawabi da ya yi dangane da sace dalibai 333 da Boko Haram su ka yi ikirarin daukar nauyi, Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya koma ya dauko kundin alkawurran da ya daukar wa ‘yan Najeriya a lokacin kamfen, sannan ya kwatanta su da abin da ke faruwa a halin yanzu.

CAN ta kara da cewa, irin tabarbarewar tsaro da ya mamaye kasar nan, hakan na nuna cewa “motar Alpha ya rubta da ‘yan Najeriya baki daya a cikin rami.”

Cikin takardar da Kakakin Yada Labarai na CAN Adebayo Oladeji ya fitar ga manema labarai, ya bayyana abin da ya faru a Kankara wani babban ibtila’i ne wanda zai kasance cikin kundin tarihin abubuwa masu muni kasar nan.

“ Kasancewa sace daliban su 333 da aka yi a ranar da Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya na cikin jihar ta sa ya fara hutun mako daya, hakan kawai ya isa ishara ga Buhari cewa ba shi da shugabannin tsaron kawai.

“ Arcewa da yaran da aka yin a nufin gwamnatin Najeriya da shugabannin tsaron kasar ba su dauki wani kwakkwaran darasi ba daga sace dalibai mata 276 a Chibok ba, cikin 2014 a Jihar Barno. Kuma ba su dauki darasin komai ba a kan abin da ya faru da daliban GGSTC Dapchi, cikin Jihar Yobe, a 2018 ba.”

“Hakan kuma na nufin masu ruwa da tsaki kan harkokin ilmi sun bi sahun jami’an tsaro, su ma ba su koyi darasin komai ba daga abin da ya faru da dalibai a Chibok da da Dapchi ba. Ga shi abin baki har yau ba a ceto sauran daliban Chibok ba, kuma ba a ceto sauran dalibar Dapchi ba da ta rage, wato Leah Sharibu daga hannun ’yan ta’adda.

“Duk irin wadannan abubuwa ne mu ka hanga a baya da muka rika matsa wa Buhari lamba da caccaka, muna kira ya tsige shugabannin bangarorin tsaron sa. Amma da ya ke kunne-kashi gare shi, ba ya sauraren shawara daga mutane masu hangen-nesa.” Inji CAN.

Share.

game da Author