A bidiyo da Boko Haram suka saki ranar Alhamis, Ya nuna yaran makarantan Kankara suna rokon jami’an tsaro su daina yi wa Boko Haram shawagi ta sama a jiragen yaki.
Daya daga cikin daliban da yayi magana, ya ce jami’an tsaron Najeriya ba za su iya yi wa Boko Haram komai ba, saboda haka su din kokarin afka musu.
Daga nan sai sauran daliban wanda yara ne kanana suka rika cewa da kukan a zo a cece su.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Boko Haram suka sace daliban makarantan Kankara su 333 a garin kankara.
Sai da suka dauki tsawon awa 5 cur suna kwashe yaran makarantan a cikin kankara kafin suka tafi da su.
Ana cigaba da gudanar da zanga-zanga a Kankara na kira ga gwamnati ta dawo da yaran makarantan.
Wasu daga cikin iyayen yaran sun ce ba za su koma gida ba sai an sako musu ƴaƴansu kafin su koma gida.