Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin daurin shekaru bakwai da wata kotu ta yi wa tsohon Kakakin Yada Labarai na jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, bisa kama alkalin da ya yanke masa hukuncin da nuna bangaranci a shari’ar.
Manyan Alkalai uku a Kotun Daukaka Kara sun hakkake cewa alkalin da ya daure Olisa Metuh daurin shekara bakwai a kotu, bai yi masa adalci ba, saboda ya nuna bangaranci.
An dai daure shi shekara bakwai ne a gidan kurkuku a cikin watan Fabrairu, 2020.
Babban Mai Shari’a Stephen Adah shi ne ya jagoranci sauran alkalai biyu, wadanda su ka soke hukuncin da aka yi wa Metujh, tare da cewa a sake shari’ar daga farko.
Sun bada hukuncin cewa a maida shari’ar ga kowane Alkalin Babbar Kotun Tarayya, amma banda mai shari’a Okon Abang, wanda ya daure shi shekaru bakwai.
Babban Mai Shari’a Adah a Kotun Daukaka Kara, ya ce “irin furucin da Abang ya rika yi a lokacin hukunta Metuh, duniya ta tabbatar da cewa ya na kullace da shi kua ziciyar sa cike ta ke da nifaka a kan Metuh.”
Ya ce bai kamata mai shari’a ya goyi bayan wani bangare ba a wajen yanke hukunci. Abin kuma inji shi, rashin adalci ne karara.
Ya kara da cewa irin wannan cin kashi da rashin mutunci da alkalai ke yi, ba abin da za a ci gaba da zura ido ba ne na faruwa a kasar nan.
Ya ce rashin adalci ne mai shari’a ya tauye wa wanda ake wa shari’a hakkin sa ta hanyar nuna masa bambanci da bangaranci.
Adah ya kara da cewa Mai Shari’a Abang ya zubar da kima da martabar kotu a idon duniya. Saboda haka ba za a kyale hukuncin da ya yi wa Metuh ya zama karbabbe ba.