Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawan zai sake gurfana a kotu domin wata sabuwar tuhuma kan cuwa-cuwar naira milyan 500 da sunan ladar yanke ciyawa a sansanin ƴan gudun hijira.
Babachir wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Tarayya na farko da Buhari ya nada a farkon zango na biyu, an tsige shi bayan kafafen yada labarai sun takura wa Buhari dangane da biris din da ya yi a kan harkallar.
Za a gurfanar da shi tare da wasu mutum shida, wadanda su ka hada da Hamidu Lawal, Suleiman Abubakar, Apeh Monday, sai wasu kamfanoni biyu.
A gurfanar da su ka yi gaban Mai Shari’a Jude Okeke na Babbar Kotun Tarayya a Abuja a ranar 13 Ga Fabrairu, su duka shida din sun musanta akwai hannun su a harkallar.
An dage shari’ar zuwa 19 Ga Maris, 2019, amma sai mai gabatar da kara ya nemi a ba shi lokaci ya yi gyare-gyare a cikin tuhomi 10 da ake yi masu.
Daga nan aka samo tsaikon shari’ar, ba a sake komawa ta kan ta ba, kisan watanni 9 da su ka gabata.
An sanar da mutuwar mai shari’ar cikin watan Agusta, a daidai lokacin da EFCC ke kokarin gayyatar wadanda za su bayar da shaida.
Alkalin ya rasu a Asibitin Kasa da ke Abuja, daga nan kuma sai aka maida shari’ar a kotun Mai Shari’a Charles Agbaza ke Babbar Kotun FCT a Jabi.
An gurfanar da su a ranar Litinin, inda a can ma su ka musanta hannayen su a harkallar.
Mai Shari’a Agbaza ya aza ranar 20 Ga Janairu, 2021 domin fara shari’ar tun daga farko.