FADIN GASKIYA: An rage wa Babban Kwamandan Yakin Boko Haram Janar Adeniyi mukami

0

Kotun Sojoji mai tuhumar jami’an ta a asirce, ta yanke Manjo Janar Olusegun Adeniyi hukuncin rage masa mukami, inda aka maida shi baya tsawon shekaru uku.

Hukuncin na nuni da cewa sai nan da shekaru uku Adeniyi zai sake kai mukamin da ya ke a yanzu.

An yanke masa hukuncin ne saboda ya fito a soshiyal midiya ya fitar da bidiyon da ake nuna shi ya na korafin rashin wadatattu da ingantattun kayan fada da sojoji ba su da shi, balle har su rika yin galaba kan Boko Haram.

Lamarin ya faru lokacin da Adeniyi ke Babban Kwamandan Operation Lafiya Dole, a Jihar Yobe, bayan wani artabu da Boko Haram su ka yi wa sojoji kwanton-bauna su ka kashe soja 43.

A cikin bidiyon mai nuna halin da sojojin da ke yaki da Boko Haram su ka tsinci kan su, Adeniyi ya rika yin korafin yadda Boko Haram su ka yi masu kwanton-bauna, su ka kashe sojoji birjik.

Am rika nuno shi ya na magana a tsakiyar sojoji na kasa da shi, wadanda su ka kwaci kan su da kyar a hannun Boko Haram.

Adeniyi ya bayyana yadda sojojin su ka afka cikin tarkon kwanton-baunar da mayakan Boko Haram su ka yi masu har su ka bude masu wuta.

Ya kuma yi korafin cewa akwai magulmacin da ya sanar da Boko Haram lokacin da sojojin za su wuce.

An rika nuno Adeniyi ana nuno bidiyon hoton barnar da Boko Haram su ka yi wa sojojin, wadanda Manjo Janar Adeniyi ya ce an zagaye su da manyan motocin yaki za su kai 15.

Da ake yanke masa hukunci a ranar Litinin a Abuja, an shaida masa cewa ya karya dokar soja ta watan Yuni, 2018, wadda ta haramta wa soja fitowa a fili ko a soshiyal midiya fitowa su yi korafin wata matsalar da ta dame su, wadda ya shafi tsakanin su da gwamnati ko hukumar sojojin kasar nan.

Akan wannan aka rage masa mukami, tare da maida shi baya tsawon shekaru uku.

Shi kuma wani hadimin sa, wanda kurtun soja ne, karabiti, an yanke masa daurin kwanaki 28, tare da tilasta shi yin aikin karfi wurjanjan a lokacin da ya ke a daure.

An maka masa wannan hukunci ne saboda daukar bidiyon da ya yi.

An kama Adeniyi da wannan laifin fitowa a soshiyal midiya ya watsa bidiyon da ake ganin ya zubar da kimar Najeriya, watanni hudu bayan Najeriya ya jinjina masa, saboda kakari da jajircewar wajen yaki da Boko Haram.

Share.

game da Author