KANJAMAU: Dalilan da suka sa Najeriya bata iya kaiwa ga kawar da cutar a 2020 ba

0

Bayyanar Annobar korona ya kawo koma baya a fannin kiwon lafiya inda hakan ya hana Najeriya cin ma burinta na kawar da kanjamau a 2020.

Kafin bayyanar cutar korona Najeriya na fama da matsaloli na rashin mai da hankali wajen hana haihuwan jarirai da cutar, samar wa masu masu yin mu’amula da tarayya na jinsi daya, karuwai da masu yin ta’ammali da miyagun kwayoyi maganin cutar wanda haka ke sa ba a samun raguwar yaduwar cutar a kasar nan.

Sai dai kuma duk da haka Najeriya ta samu wasu nasarori a yakin da take yi da cutar a kasar.

Idan ba a manta ba a shekaran 2014 humar majalisar dinkin duniya, UNAIDS ta tsara wasu hanyoyi da shirye-shiye da ta yi wa taken ’90-90-90 strategy’ domin dakile yaduwar cutar daga wannan lokacin zuwa 2030.

Wannan shiri ya hada da yi wa akalla kashi 90 bisa 100 na mutanen dake dauke da cutar gwaji, samar wa kashi 90% magani sannan da tabbatar da cewa kashi 90% na amfani da maganin yadda ya kamata domin ganin an samu nasarar rage kwayoyin cutar a jikin su.

Bayan shekaru biyu da haka shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci a tsananta yin gwajin cutar domin taimakawa wajen samun nasarar wannan shiri na ’90-90-90 strategy.

A wannan rana ta 1 ga Disamba, wacce rana ce da aka kebe domin cutar Kanjamau a Duniya PREMIUM TIMES HAUSA ta zakulo wasu matsaloli dake hana a samu nasara a yaki da kanjamau da ake yi a kasar nan.

Sanin adadin yawan mutanen dake dauke da cutar

Daya daga cikin matakan dakile yaduwar cutar da gwamnati ta dauka shine sanin adadin yawan mutanen dake dauke da cutar.

Gwamnati tare da hadin gwiwar hukumar NAIIS sun gudanar da binciken a Maris din 2018 sannan aka gabatar da sakamakon binciken a 2019.

Gwamnati ta kashe dala miliyan 100, ta dauki ma’aikatan 185 sannan an samu mutum sama da 200,000 dake dauke da cutar a kasar nan.

Sakamakon binciken ya nuna cewa mutum miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar a Najeriya sannan an samu nasaran rage akalla kashi 40% na yaduwar cutar.

Kwararrun ma’aikatan lafiya sun ce sakamakon binciken zai taimaka wajen tsara hanyoyin da za su fi dacewa wajen dakile yaduwar cutar domin cimma burin ’90-90-90 strategy’.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce a dalilin wannan bincike da aka yi ya sa an gano cewa kashi 60 na mutanen dake dauke da kanjamau ne ke samun magani a kasar nan.

Rashin hadawa da karuwai, masu yin mua’amula da jinsi iri daya da ta’ammali da miyagun kwayoyi na daya daga cikin dalilan da ya sa ba aiya samun hakikanin gaskiyar yawan wadanda suka kamu da cutar.

Wadannan rukunin mutane sun fi kowa zama cikin hadarin kamuwa da cutar domin kwaso mai yawa na mazan dake yin luwadi kadai sun kamu da cutar.

Baya ga kasar Afrika ta Kudu Najeriya ce ƙasa ta biyu a kasashen Afrika da cutar ta yi wa katutu.

Haihuwar jarirai da cutar kanjamau

Najeriya na daya daga cikin kasashen duniyan da ta fi samun yawan jariran da ake haihuwa sun kamu da cutar kanjamau.

Bincike ya nuna cewa a shekaran 2016 an haifi jarirai da suka kamu da cutar kanjamau 37,000 a Najeriya sannan a duniya kuma jarirai 160,000.

Kasar Afrika ta Kudu da yaduwar kanjamau ya fi tsanani a wannan shekara jarirai 12,000 aka haifa sun kamu da cutar.

Shugaban hukumar dakile yaduwar cutar kanjamau na kasa NACA Gambo Aliyu ya ce yi wa mata gwajin cutar a kauyuka da sauran wurare ne mafita.

Ya ce a yanzu haka gwamnati ta dauki wannan mataki sannan tana kokarin jawo hankalin gwamnati jihohi suma su maida hankali akan haka domin a rage yawan haihuwan jarirai da suka kamu da cutar.

Annoban Korona

Bullowar cutar korona ya dawo da hannun agogo baya a Najeriya.

Korona ta hana masu fama da kanjamau samun magani da kulan da ya kamata inda a dalilin haka wasu kwararrun ma’aikatan lafiya ke fargaban cewa za a samu karuwan yawan wadanda za su kamu da kuma wadanda zasu mutu a dalilin haka.

Sannan kudaden da ada aka ware su don aikin cutar Kanjamau sai aka karkatar dsau zuwa yaki da korona.

Wata jami’ar UNAIDS Winnie Byanyima ta ce hakan da gwamnati ta yi bai dace ba.

Nuna wariya

Nuna wa masu dauke da kanjamau wariya na sa ba su samun aiki, an kori wasu daga aiki, an ci zarafin wasu, wasu kuma basu samun kula a asibiti da sauran su.

PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa duk da ci gaban da aka samu har yanzu akwai mutanen da basa iya fadi cewa suna dauke da kanjamau.

Shugaban kungiyar ‘Christian AID’, Charles Usie ya ce nuna wariya na hana mutane yin gwajin da hana masu fama da cutar zuwa amsar magani sai su yi boye-boye saboda tsoron wulakanci da kyamatar su.

Bincike ya nuna cewa kawoyin cutar na raguwa a jikin mutum idan har yana shan magani yadda ya kamata.

Sannan gwamnati ta kafa dokar hukunta duk wanda ke nuna wa masu duke da Kanjamau wari ko kuma kyamatar su.

Ware kudade domin yaki da cutar

Shugaban Hukumar NACA, Gambo Aliyu ya ce tsakanin 2005 zuwa 2018 Najeriya ta kashe dala biliyan 6.2 wajen kula da kashi 60% na masu fama da kanjamau.

Kashi 70 na wadannan kudade da aka kashe sun fito ne daga aljihan kungiyoyin bada tallafi.

A yanzu haka wannan tallafi da kungiyoyin ke badawa sun fara raguwa kuma gwamnatin Najeriya har yanzu bata tsara wasu hanyoyin da za a ce za a bi ba don cigaba da kula da masu cutar ko da tallafin ya yanke.

Kwararrun ma’aikatan lafiya sun yi kira ga gwamnati da su bude masana’antu domin hada maganin kanjamau a kasar nan.

Bayan haka Aliyu ya ce gwamnati ta bude asusu domin Tara kudaden da za a bukata wajen siyo maganin cutar.

Ya ce kudaden asusun zai taimaka wajen siyo Kashi 40% na maganin cutar.

Karuwai, ‘Yan luwadi da masu ta’ammali da muggan kwayoyi

A Najeriya gwamnati ta kafa dokar daure duk wanda aka kama yana ludu, za a daure shi na tsawon shekaru 14 sannan wanda ke mara wa irin wannan harka baya za a daure shi na tsawon shekaru 10.

A dalilin wannan doka masu ludu musamman wadanda suka kamu da kanjamau sun boye kansu ba a san da su ba ballantana har su amshi magani.

Koda ya ke dokar kasar nan ya nuna cewa kowa na da ‘yancin samun maganin kanjamau amma masu ludu sun gwammace su boye kansu cutar ta kashe su.

Rashin sani

Wani binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa har yanzu akwai matsalar rashin sani game da cutar kanjamau a tsakanin mutane.

Wasu da dama basu san suna dauke da cutar ba kwata-kwata. Wannan shima matsala ne babba dake maida hannun agogo baya,

Matakin da aka dauka domin cin ma burin kawar da cutar

A watan Yuli hukumar UNAIDS ta ce kawar da cutar nan 2020 zai yi wahala saboda matsaloli kamar nuna wa mutane wariya da dai sauran su. Hukumar ta ce tabbas sai an kau da wadannan matsaloli kafin a iya kaiwa ga cimma burin kauda cutar a kasashen duniya.

Share.

game da Author