Buhari ya bude boda

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a bude kan iyalolin kasar nan hudu, sai kuma har yanzu bai amince a ci gaba da shigo da shinkafa daga kan iyakokin Najeriya ba.

Sanarwar wadda Ministar Harkokin Kudi, Zainab Ahmed ta sanar wa manema labarai bayan tashi daga taron Majalisar Zartaswa na yau Laraba a Fadar Shugaban Kasa, ta ce amma har yanzu haramcin shigo da shinkafa, kaji da sauran kayayyakin da aka shigowa na nan, ba a janye ba.

Kan iyakokin da aka amince a bude, sun hada da Seme da ke Lagos zuwa Kwatano, ta Ilela da ke kan iyakar Sokoto da Jamhuriyar Nijar, ta Maigatari da ke kan iyakar Jigawa da Jamhuriyar Nijar, sai kuma ta Mfun da ke kan iyakar Kudu Maso Kudu.

Shugaba Buhari ya halarci taron ta talbijin, daga gidan sa a Daura inda ya ke hutun mako daya.

Sanarwar ta ce yayin da za a bude kan iyakokin hudu nan take, sauran iyakokin kuma za a bude su kafin ko a ranar 31 Ga Disamba, 2020.

Buhari dai na Daura inda ya ke hutun mako daya, yayin da ya ke kan shan matsin-lambar cakkakar da ake yi masa kan sace daloban sakandare na makarantar kwana ta Kankara cikin jihar, su 333 da Boko Haram su ka yi ikirarin sace wa.

Share.

game da Author