An ci gaba da shari’ar wani hatsabibi kuma tantirin malamin tsibbu mai suna Jamiu Isiaka, wanda ya yi amfani da sunan Kakakin Shugaba Buhari, Femi Adesina da tsohon Shugaban Hukumar NNPC, Maikanti Baru, ya taki sa’a ya damfari wani dan kasar Koriya ta Arewa naira milyan 30.
An ci gaba da shari’ar ce a ranar 15 Ga Disamba, wadda Hukumar EFCC ta gurfanar da shi. A ranar an gabatar da mai shaida, Dare Folarin.
Bokan wanda ba dattijo ba ne, shekarun sa 31, ya rika bayyana wa wadanda ya ke so ya damfara cewa shi wani babban jami’in gwamnatin Najeriya ne, ya damfari dan Koriya ta Kudu kudi naira milyan 30, a bisa alkawarin cewa zai samo masa fam wanda zai rike a matsayin shaidar satifiket da zai rika samun kwangiloli a kamfanin mai na NNPC.
Fam din zai ba shi dama da amincewar gwamnatin Najeriya ya rika sayen danyen man fetur daga nan Najeriya.
A wurin bincike dai boka Isiaka ya ce ya yi amfani da kudin ne ya tanadi kayan da ya yi wad an Koriya din surkulle, kulumboto da ’yan tsatsube-tsatsuben samun sa’a.
Daga cikin kayayyakin sinadaran surkulle, kulumboto da tsatsube-tsatsuben da bokan ya tanadar, akwai jibgegiyar ungulu, kan wani gazagurun zaki, tafkekiyar fatar giwa, tulin hanjin giwa da kuma hantar gatan-biri.
Tun a ranar 14 Ga Yuni, 2019 ne dai Ofishin EFCC na Shiyyar Ilorin ya gurfanar da bokan a gaban Mai Shari’a Mahmood Abdulgafar na Babbar Kotun Ilorin, bisa zargin sa da aikata laifuka hudu da su ka hada da yin damfara ta hanyar sojan-gona da fojare,
Kotu a lokacin ta ki amincewa ta bada belin sa, sai aka tura shi kurkuku da Mandala.
Yayin da ake shari’ar, EFCC ta damka wa kotu takardu wadanda ta gabatar a matsayin shaidu.
Daga nan EFCC ta kammala gabatar da shaida, aka bada fili ga wanda ake tuhuma ya ci gaba da fara kare kan sa.
Ana kan haka sai EFCC ta samu gulmar wata barankyankyama, wadda ta gaggauta neman kotu ta kara mata lokaci domin ta kara antaya wasu hujjojin irin damfarar da boka Isiaka ya tafka.
A ranar 15 Ga Disamba dai lauyan EFCC, O.B Akinsola ya shaida wa kotu cewa binciken su ya gano Isiaka ya saki manyan gidaje da kudaden da ya damfari Keun Sig Kim a cikin Ilorin.
Mai gabatar da kara ya shaida wa kotu cewa sun ma gano fili ne Isiaka ya saya a hannun Alfa Jami’u a unguwar Oke-Fomo, sannan ya gina makeken gida duk da kudaden da ya damfari Kim.
Bayan damka wa kotu hoton gidan, Mai Shari’a Abdulgafar ya daga karar zuwa ranar 21 Ga Janairu domin wanda ake tuhuma ya kare kan sa.