Akwai yiwuwar Najeriya ta samu maganin Korona a watan Janairu – Minista Ehinare

0

Ministan Lafiya, Osagie Ehinare ya bayyana cewa akwai yiwuwar Najeriya ta samu maganin rigakafin Korona a cikin watan Janairu mai zuwa.

Ehinare ya ce dama kuma tuni kasar ta shiga yarjejeniya da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, da kamfanin Gavi da zaran maganin ya fito za a wadata Najeriya da shi.

Sai dai kuma bai fadi yawan maganin da za a siyo ba.

” Muna sa ran cewa za mu samu maganin, komai kankanta shi, domin suma kasashen da ke hada maganin na bukatarsa.

Baya ga siyo maganin da za a yi, tsadar sa shima wani abinda za mu duba ne. Sannan kuma wajen ajiya. Maganin na bukatar wajen ajiya mai san karan sanyi wanda mu a kasar nan bamu da irin wadannan na’ura.

Ehinare ya ce shi kansa wurin ajiyan sai an siya.

” Akwai maganin da za mu iya ajiye a firjin mu, da wadanda za mu siyo mu saka su a ciki, sai dai wadanda ke bukatan a ajiye su cikin firji mai dankaran sanyi sai dole an siyo su wadannan firji, Su ma kuma tsadan tsiya suke da shi.

Ya ce gwamnati za ta garzaya wasu kasashen da ke hada maganin domin a siyo su da yawa domin mutanen kasa.

Share.

game da Author