An gano wani gwamna dake da hannu dumu-dumu wajen ruruta wutan Ta’addanci a yankin Arewa Maso yamma -Inji APC

0

Jam’iyyar APC ta zargi wani gwamna cikin gwamnonin yankin Arewa Maso Yamma da hannu dumu-dumu a hare-haren da yankin ke fama da shi.

Jam’iyyar bata bayyana sunan gwamnan ba ko kuma jam’iyyar sa, amma ta ce bincike mai zurfi da aka yi ya nuna cewa gwamnan na mu’amula da ƴan ta’adda sannan kuma shi ya ke dawainiya da su, ya na kashe musu kudi.

” Bincike mai zurfi da jami’an tsaro su ka yi ya tabbatar da hannun wani gwamnan yankin Arewa Maso Yamma da ke cika wa ƴan ta’adda aljihu da kudi kuma yana daukar nauyin ta’addancin da hare-haren ‘yan bindiga da ke gallaza a wa mutanen yankin Arewa azaba.

Jam’Iyyar APC ta ce bayanan sirri sun tabbatar da hannu wannan gwamna kuma zuwa yanzu ana ci gaba da bincike domin bankado wasu kulle-kullen na sa.

Bayan haka jam’iyyar ta yi kira ga jami’an tsaro su gaggauta daukan mataki akan wannan gwamna domin abinda yake yi ya wuce gona da iri yanzu.

Sannan kuma ta ce ta gano cewa burin wannan gwamna shine ya tarwatsa yankin Arewa Maso Yamma. Yana amfani da yan ta’adda da mahara domin kawo rashin zaman lafiya a yankin sannan kuma yana narka makudan kudi ga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda su ci gaba da gallaza wa mutanen yankin azaba.

Share.

game da Author