Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana yadda gwamnati da makarrabanta suka ceto yaran makarantan Kankara da masu garkuwa da mutane suka arce da su.
A hira da yayi da DW ta Jamus, Masari ya ce an hada da jami’an tsaro da wasu jami’an gwamnati wajen tattaunawa da masu garkuwan har aka iya ceto su.
” Sannan kuma ko sisi gwamnati bata ba su ba, tattaunawa ta yi da su har aka cimma matsaya suka saki yaran.
Masari ya kara da cewa ba Boko Haram bane suka sace yaran, yan bindiga ne tsangwararan suka tafi da yaran cikin daji.
Ya kuma kara da cewa za a kai taho da yaran garin Katsina domin likitoci su duba su sannan kuma sannan a basu kayan sawa su canja na jikin su. Daga nan sai a mika su ga iyayen su.
Akalla yaran makaranta sama da 300 ne ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su.