Kamfanin hada magunguna na ‘Gavi Vaccine Alliance’ ya bayyana cewa, sakamakon wani bincike da kamfanin ya yi ya nuna cewa yara kanana na da garkuwar jiki mai karfin da zai kare su daga kamuwa da Korona.
Sakamakon binciken ya nuna cewa yara sun fi manya garkuwar jiki mai karfi da zai kare su daga kamuwa da cutar.
Binciken ya fi bada karfi wajen gano yadda garkuwar jikin ke iya kare yara daga kamuwa da cutar.
Sakamakon binciken da aka yi
Sakamakon binciken ya nuna cewa sinadarin ‘spike protein’ shine garkuwar jikin dake Samar da kariya daga kamuwa da korona a jikin mutum.
Sannan kuma ba kowani mutum ne ke dauke da wannan sinadari domin cikin mutum 302 din da aka gudanar da binciken akan su, kashi biyar ne cikin wadannan mutane ke da irin wannan sinadarin dake karfafa garkuwar jiki.
Binciken ya gano cewa za a fi samun irin wannan kariya a jikin yara masu shekaru 6 zuwa 16, sannan kuma shi wannan sinadari wato ‘spike protein’ ya kasu lashi biyu ne. Akwai S1 da S2.
An gano cewa S2 ce ta fi karfi wajen samar wa mutum kariya daga kamuwa da cutar.
A dalilin haka kamfanin ke ganin ya kamata masu hada maganin rigakafin korona su yi amfani da irin wannan sinadarin wajen hada maganin.