Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 82 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –48, Rivers-8, Kwara-6, Yobe-6, Katsina-5, FCT-3, Nasarawa-2, Filato-1, Ogun-1, Kano-1 da Osun-1
Yanzu mutum 67,412 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 63,055 sun warke, 1,173 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,184 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 23,238, FCT –6,770, Oyo – 3,721, Edo –2,696, Delta –1,824, Rivers 2,985, Kano –1,795, Ogun –2,223, Kaduna –3,064, Katsina -1,030, Ondo –1,728, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi –770, Ebonyi –1,055, Filato -3,858, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –662, Jigawa – 331, Kwara –1,102, Bayelsa – 445, Nasarawa – 493, Osun –946, Sokoto – 165, Niger – 298, Akwa Ibom – 339, Benue – 496, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 100, Ekiti – 365, Taraba- 159, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
Domin samun ingantattun bayanai game da korona a Najeriya gwamnati tare da hadin guiwar UNICEF sun samar da wata layin kira na waya da za a rika samun labarin gaskiya game da cutar.
Mutum zai aika da sakon ‘Coronavirus’ zuwa lambar 24453, daga nan za a aiko masa da sakonni game da cutar da matsayin da duniya ke ciki da kasa Najeriya.
Domin shiga wannan dandali a facebook ko Kuma WhatsApp za a iya aikawa da sakon ‘Coronavirus’ zuwa ga +234 908 740 1607. Ko Kuma ta adireshin U-Report kamar haka @ureportnigeria
Wakilin asusun UNICEF a Najeriya Peter Hawkins ya gargadi mutane da su cigaba da kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar korona cewa yin haka ne kadai mutum zai iya samun kariya daga corona.