Cikin makon da ya gabata an tabbatar da kisan mutum 86 a fadin Najeriya, tare da yin garkuwa da mutum 9, baya ga kisan yankan ragon da Boko Haram su ka yi a wasu wurare.
Wannan shi ne iyar adadin kashe-kashe da garkuwar da kakafen yada labarai su ka iya tattara kawai.
Duk da Fadar Shugaban Kasa ta saba karyata yawan kashe-kashen da ake bayar da rahoto, mambobin Majalisar Tarayya sun yi tir tare da nuna damuwa kan yawaitar kashe-kashe da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a kasar nan, musamman a arewacin Najeriya.
Sau da dama Fadar Shugaban Kasa na musanta yawan wadanda ake kashewa. Amma a gefe daya Majalisar Tarayya na nuna danuwa da yin tir da yawan hare-haren.
PREMIUM TIMES Ta tattaro wasu rahotannin da aka bayan a cikin makon da ya gabata, wadanda suka bayyana adadin yawan mutanen da aka kashe, sai kuwma yawan wadanda aka yi garkuwa da su a cikin makon da gabata.
Ranar Lahadi
Ranar Lahadin makon jiya ce ‘yan bindiga su ka yi wa Shugaban Jma’iyyar APC na jIhar Nasarawa, Philip Shekwo tattaki har gida, su ka yi awon gaba da shi.
Sun shiga gidan bayan sun bude wa mai gadi wuta, su ka haura ta Katanga. An ce sun isa wurin runduna guda kamar za su yaki.
Sa’o’I kadan bayan sace shi, an tsinci gawar Shekwo, kamar yadda iyalin sa da jam’iyyar APC ta jiha da kuma ta kasa su ka tabbatar.
Duk a waccan rana ce wani gigitaccen dan sanda ya bude wuta a bangaren mashayar da ke cikin wani otal, daidai lokacin da ake kallon kwallo, har ya kashe mutum daya kuma ya ji wa daya mummunan rauni a kafar sa.
Haka kuma masu garkuwa da mutane su ka mamaye masallata a cikin wani masallaci a cikin Karamar Hukumar Maru ta jihar Zamfara, inda su ka kashe mutum biyar. Rahotanni sun ce an yi garkuwa da mutum 30, cikin su har da Limani. ’Yan sandan Zamfara sun tabbatar da kisan da yiin garkuwar, amma ba su fadi yawan wdanda aka tasa keyar ta su cikin daji, aka yi garkuwar da su ba .
Bayan haka, an tabbatar da kisan tsohon shugabankaramar hukumar Sabuwa ta cikin Jihar Katsina, mai suna Lawal Dikko. Mahara ne shi ma su ka bindige shi.
Shugaban Jam’iyyar PDP jihar Katsina, Salisu Majigiri ne ya tabbatar da kisan ga manema labarai.
A waccan rana ce dai mahara su ka kai hari a gidan Mamba na Majalisar Tarayya, mai wakiltar Kananan Hukumomin Kusada/Ingawa/Kankiya, Hon. Abubakar Yahaya. Sun arce da dangin sa mutum biyu.
Ranar Litinin
PREMIUM TIMES Ta ruwaito yadda Boko Haram su ka kashe sojojin Najeriya shida, su ka jikkata 26 tare da neman wasub sojojin masu yawa, amma ba a san inda su ke ba.
An kai wa sojojin wannan mummunan hari a Jagiran da Monguno, Jihar Barno.
Bayan wannan kuma sai da su ka kwaci Toyota Land Cruiser SUV, wadda harsashi ba ya huda ta a hannun sojojin.
Haka kuma wannan jarida ta ruwaito yadda wani likita mazunin Jihar Kogi mai suna Azubuike Iheanacho ya fada hannun masu garkuwa da mutane, da ke zaune a Karamar Hukumar Dekina.
Jaridar The Cable ta buga wani labarin yadda masu garkuwa da mutane su ka yi garkuwa da wani malamin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, mai suna Bako. An kuma arce da matar sa da ’yar sa.
Kakakin ABU Mai suna Awwalu Umaru ya tattabar da sace malamin da iyalin sa, a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ita ma Sahara Reporters ta buga labarin sace Tofai Nanono, dan uwa ga Ministan Harkokin Noma Sabo Nanono. An sace shi a kauyen Tofai cikin Karamar Hukumar Gabasawa ta Jihar Kano. Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna ya tabbatar da faruwar Lamarin.
Ranar Talata
Hukumomin Tsaron Najeriya sun tabbatar da kashe Boko 22 da Dakarun Operation Lafiya Dole su ka yi a jihar Barno a Ngamdu.
Ranar Laraba
A wannan rana masu garkuwa sun shiga cikin al’ummar Yolde Pate da ke cikin Karamar Hukumar Yola ta Kudu, su ka kama matar wani jami’in dan sanda tare da dan sa daya.
Alhamis
Bayan bindige mutum uku da wurare biyu daban-daban da ‘yan bindiga su ka yi a jihar Ondo, sun kuma harbi mutum biyu a garin Ode-Irele da ke Karamar Hukumar Ilere. Lamarin ya faru lokacinn da masu fashi su ka kai hari wani banki da ke kusa da ofishin ‘yan sanda.
Ranar Juma’a
An sace matar Olugbenga Ale, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Ondo. Amma an sake ta a washegari ranar Asabar.
Ranar Asabar
Wannan jarida ta buga labarin kashe manoman shinkafa su 44 da Boko Haram su ka yi wa yankan rago Garin Kwashebe, jihar Barno.
An yi masu kisan gilla a lokacin su ke aikin gona, a ranar da ake gudanar da zaben karamar hukuma.