‘Yan Sandan Najeriya ba su bukatar garambawul, a gyare su ke – Minista Malami

0

Yayin da ‘yan Najeriya ciki har da Shugaba Muhammadu Buhari su ka gamsu da kiraye-kirayen a sauya fasalin ‘yan sandan Najeriya, har ta kai aka rusa SARS, shi kuwa Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami cewa ya yi, “yan sandan Najeriya a gyaren su su ke, ba su bukatar wani gyara.”

Zanga-zangar #EndSARS da ta samo asali daga azabtarwa da kisan jama’a da rundunar SARS su ka rika yi, ta haifar za zamamar tarzomar da ta ci rayuka 50, ciki har da na ‘yan sanda 22, da asarar dimbin dukiyoyi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya amsa bukatu biyar na masu zanga-zanga, ciki har da rusa rundunar SARS, aka maye gurbin su da SWAT.

Duk da hakan shi kuwa Ministan Shari’a Malami na cewa ba su bukatar wani garambawul.

Hujjar Minista Malami:

“Shin wane garambawul ku ke so a yi wa ‘yan sanda ne? Mene ne aibin jami’an da su ka kyale masu tarzoma su ka kona masu ofisoshi har sama da 200, amma kuma ba su harzuka sun afka wa masu tarzoma ba?”

“In ina ganin jami’an tsaron nan su na da hankaki, kyawon dabi’a, kauda kai daga aikata munanan ayyuka kan jama’ kamar yadda dokar kasar nan ta shimfida.” Inji Malami.

Malami ya kara da buga misali da yawan ‘yan sandan da masu tarzoma su ka kashe.

Ya nuna cewa shekaru 20 a kasar nan ba a taba yi wa jami’an ‘yan sanda mummunar barna irin wannan lokaci ba, amma hakan bai harzuka ba, bai kuma tunzura su har su ka afka wa masu tarzomar kashe su, banka wa ofisoshin su wuta da kwasar kayan jama’a ba.

Malami ya yi wannan jawabi ne a taron ganawa da ‘yan jaridu na duniya a dakin taro na Fadar Shugaban Kasa, wanda bangaren masu yada labarai na Shugaba Buhari su ka shirya taron, ranar Litinin a Abuja.

Malami ya jinjina wa Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa kan yadda ta nuna dattako da kwarewar iya aiki da juriyar da ta ki afka wa masu tarzoma, duk da mummunar barnar da aka yi wa jami’an.

Share.

game da Author