Kaddara ce ta fado kaina, amma ina rokon ku ku yi hakuri, hakan ba zai sake faruwa ba – Rahama cikin ‘Hawaye’

0

Rahama Sadau ta roki daukacin musulman duniya da duk wani dan Najeriya Musulmi ayi hakuri kan yadda hotonta ya janyo cece-kuce da izgilanci tsakanin masu bita a shafukan ta na yanar gizo.

A wani bidiyo da ta saka a shafinta ta Instagram da yamman Talata, Rahama ta roki musulmai ƴan uwanta da abokanan aikinta, cewa lallai ta tafka kuskure kuma hakan ba zai sake faruwa ba.

” Wannan ba dabi’a ta bane a matsayina na musulma, na yi wannan bidiyo ne cikin nadama da takaici. Ina kuma mai ba da hakuri bisa abinda ya faru ga dukkan Hausawa da abokan aikina da musulmai baki daya kan wannan hoto nawa da ya jawo cece-kuce.

Rahama ta fashe da kuka cikin tausayi da natsuyi tana mai yin nadama da juyayin irin abinda wannan hoto nata ya janyo mata da addininta na musulunci.

Ta kara da cewa bata da ta cewa wai don ko ta kare kanta, kaddara ne ya afko mata a daidai ta saka wannan hoto sannan wani ya bi karkashin hoton ya rika amfani da shi ya na sukan addinin Musulunci da Annabi SAW.

Kafin ta sako wannan bidiyo mutane da dama sun rika jifarta da tsinuwa da muggan kalamai. Wasu na ganin dama ta saba nuna halin ko in kula game da kiyayewa da tsare addininta a sana’arta da dabi’unta.

Da yawa daga cikin wadanda suka kalli bidiyo dun yi fatan Allah ya shirya ta ya shirya Al’umma gaba daya.

Share.

game da Author