Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana yadda jami’an tsaro suka ceto mutum 9 da aka yi garkuwa da su a titin Abuja zuwa Kaduna.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ya sanar da haka a hira da yayi da manema labarai ranar Litini a Kaduna.
Ya ce gwamnati ta samu labarin cewa ƴan sandan dake aiki da rundunar ‘Operation Thunder Strike (OPTS)’ ne suka ceto mutanen.
Aruwan ya ce bayan jami’an tsaron dake aiki a Akilubu-Gidan, wani gari dake gefen titin Kaduna zuwa Abuja sun samu labarin datse titin da mahara suka yi, basu yi wata-wata sai suka dira wannan wuri, wanda da misalin Karfe 4 na yamma ne.
Kafin jami’an tsaron sun isa wurin maharan sun tare wata mota kira bus dake daukan mutum 18.
Daga cikin wannan mota maharan sun tafi da mutum 9.
Jami’an tsaron na isowa wurin sai suka fara musayan wuta da maharan.
Jami’an tsaron sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su sai dai kuma direban bus din da fasinjan dake zaune kusa da shi sun mutu.
“Gwamnatin jihar Kaduna ta aika da sakon ta’aziya ga iyalan mutanen da suka mutu.
Aruwan ya ce gwamnatin jihar Kaduna za ta ci gaba da hada hannu da gwamnatin tarayya domin samar da tsaro a wannan titi.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Arewa masu Yamma da ke fama da hare-haren yan bindiga da garkuwa da mutane.
A ranar 15 ga Nuwamba PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda mahara suka yi garkuwa da malamin Kwalejin Kimiyya da Fasaha, ‘Nuhu Bamalli Polytechnic’ dake Zariya da wasu ‘ya’yan malamin kwalejin biyu.
Jami’in yada labarai na kwalejin Abdulallahi Shehu ya Sanar da haka yana mai cewa an sace wadannan mutane yayin da suke zaune ne a harabar kwalejin, wato gidajen su na harabar kwalejin.
Malamin da aka sace na koyarwa a fannin kere-kere sannan yaran da aka sace ‘ya’yan wani ma’aikacin kwalejin ne.