Tsadar rayuwa ta yi tsananin da ba ta yi a watanni 30 da su ka wuce -NBS

0

Hukumar Kididdigar Alkalumman Bayanai ta Kasa (NBS), ta bayyana tsadar rayuwa a Najeriya ta yi tsananin da watanni 30 baya ba a taba fuskanta ba.

NBS, wato ‘National Bureau of Statistics’, ta ce farashin tsadar rayuwa ya yi sama zuwa kashi 14.3 bisa 100 a cikin Oktoba, abin da aka rabu da gani tsawon watanni 30 da su ka gabata.

Tsadar rayuwar ta karu daga watan Satumba, wanda tsananin ya tsaya kashi 13.71 a watan Satumba.

Tsakanin Satumba zuwa Oktoba an samu karin kashi 1.54. Hakan ya nuna rayuwa ta fi tsanani tsakanin watan Satumba zuwa Oktoba fiye da tsakanin watan Augusta zuwa Satumba.

Tsananin tsaurin rayuwa na ci gaba da ta’azzara ta hanyar hauhawan farashin kayan abinci da na masarufi, tun daga lokacin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya kulle kan iyakokin kasar nan, da nufin dakile fasa-kwauri, musamman na shinkafa.

Lamarin ya kara muni yayin da barkewar annobar korona ta tsayar da komai cak a Najeriya da ma duniya baki daya.

Saboda hakan ne ya har yau tattalin arziki bai kai ga farfadowa daka dukan da korona ya yi masa ba.

A cikin rahoton, an bayyana yadda farashin kayan abinci ya yi tashin-gwauron-zabo daga kashi 16.66 cikin Satumba, ya koka 17.38 cikin Oktoba, 2020.

Kayayyakin da su ka kara masifar tsada sun hada birsdi, seralak, dankalin Turawa, doya, rogo, makani da gwaza, nama, kifi da man girke-girke.

Jihohin da su ka fuskanci tashin farashin komai sun hada Sokoto, Edo, Akwa Ibom, yayin da Oyo, Taraba da Jigawa ba su fuskanci hauwhawar farashi sosai ba.

Share.

game da Author