Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya bayyana muradin sa cewa yanzu babban abin da ya ke fata shi ne ya zama shugaban kasa ko kuma wani shahararen mai wa’azi.
Fayose ya bayyana haka a ranar Lahadi a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, yayin da ake wani shiri da shi a gidan radiyo, domin murnar zagayowar ranar haihuwar sa, tare da cikar sa shekaru 60 a duniya.
“Na yi suna, an san ni sarai, ina da habbasa wajen ganin na cimma abin da na sa a gaba. Irin jajircewar da na yi wajen ciyar da jihar Ekiti da al’ummar ta a gaba.
“Sannan yadda na cicciba mutane da yawa a kasar nan su ka zama wani abu, wadanda a baya ba su da wata hanyar zama wani abin, to duk wadannan alamomin cancanta ta ne na zama shugaban Najeriya.”
Fayose ya ce ya yafe wa dukkan wadanda su ka ci amanar sa a dajin siyasar da ya keto tare da su. Musamman wadanda su ka yi masa “tuggu da sharrin” tsige shi a kan mulki cikin 2006.
Ya ce lokacin da aka tsige shi daga gwamna ne lokacin da ba zai taba mantawa a rayuwar sa ba. Amma duk da haka, ya yafe wa wadanda su ka ci amanar sa.
“Ranar da aka tsige ni da karfin tsiya ce ranar da ba zan manta a rayuwa ta ba. Wannan abu ya sa min hawan jini. Sai da na shafe watanni uku cur, ina addu’a tare da tambayar ubangiji na laifin sa na yi.” Inji Fayose.
An tsige Fayose ranar 16 Ga Oktoba, 2006. Sai dai kuma bayan shekara takwas, Kotun Koli ta soke tsigewar da aka yi masa bayan shekara takwas a 2014.
Fayose ya ce ya yi matukar farin cikin sake zaben sa da aka yi karo na biyu.