PDP ta ce ba ta goyon bayan kulle-kullen kakaba wa soshiyal midiya takunkumi da gwamnati ke shirin yi

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ba ta goyon bayan kici-kicin da Gwamnatin Tarayya ke yi domin ganin an kafa dokar da za ta karya fukafukin soshiyal midiya a kasar nan.

Kakakin PDP, Kola Olagbondiyan ya ce PDP ba za ta taba goyon bayan saka wa soshiyal midiya takunkumi da dabaibayi ba, domin babu yin haka din a dokar Najeriya.

Ya ce kokarin da gwamnatin APC ke yi domin Majalisar Dattawa ta amince ta kakaba dokar, shiri ne na tauye wa matasa da kafafen yada labarai da kungiyoyin kare dimokradiyya hakkin magana.

Ya ce idan aka yi haka, to wata makauniyar hikima ce gwamnatin APC ke son kakabawa domin ta kashe bakin masu fallasa satar kudaden da ake yi.

Ya ce gwamnati na son ci gaba da tabbatar da rashin adalci ne kawai ta hanyar hana kowa yin magana, adawa ko korafi.

Ya ce idan aka kafa dokar, duk ma’aikacin gwamnatin da aka zalunta ba shi da inda zai kai kuka.

Cikin wannan mako PREMIUM TIMES HAUSA ta buga yaddw Gwamnonin Najeriya su ka goyi bayan Buhari ya karya fukafukin ‘yan soshiyal midiya.

Kokarin da gwamnatin Buhari me yi na kakaba wa soshiyal midiya takunkumi da dabaibayi, ya samu jinjina da goyon baya daga Gwamnonin Arewa.

Gwamnatin Buhari dai ta roki Majalisar Dattawa a kafa tsastsaurar dokar da za ta karya fukafukin soshiyal midiya.

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya ce idan aka kyale soshiyal midiya babu takunkumi, to za su iya taewatsa kasar nan baki daya.

Sai dai kuma masu adawa da shirin na ganin cewa wannan dabara da tuggu ne kawai domin kirkiro hanyar dakile masu sukar gwamnati.

Cikin shekarar da ta gabata, Majalisa ta yi fatali da wani kudiri da wakilin APC ya gabatar da nufin kafa dokar karya fukafukin soshiyal midiya.

Takamaimen wadanda gwamnatin tarayya ta fi korafi a kan su, akwai Facebook, Instagram, WhatsApp da Twitter.

A ranar Litinin gwamnonin Najeriya sun nuna goyon bayan su ga karya fukafukin soshiyal midiya, ta hanyar kakaba masu tsauraran dokokin da su ka ce ta haka ne kawai za a iya dakile watsa labaran bogi da kirkirar karairayi ana watsawa cikin al’umma.

Kungiyar Gwamnonin Arewa sun nuna wannan goyon baya ne, a cikin wata takardar bayan taron da su ka fitar ga manema labarai a ranar Litinin, bayan tashi daga taron su da Sarakunan Arewa da sauran masu ruwa da tsaki.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, kuma Gwamnan Jihar Filato, Simin Lalong ne ya sa wa takardar hannu.

A taron, sun yi tsinkaye da nazari da tsokacin yadda a cewar su soshiyal midiya ke kara yada labaran bogi, kirkire-kirkiren karairayi, kad-da-kanzon-kurege da bayanan shifcin-gizo masu haddasa fitintinu a cikin kasa.

Share.

game da Author