KASAFIN 2021: Hukumar Bada Wutar Lantarki ta Kasa za ta sayi tebura da kujerun naira bilyan 2

0

Hukumar Kayyade Wutar Lantarki ta Kasa (NERC), ta tsara yadda za ta kashe naira bilyan 2 wajen sayen kujeru, tebura da falankin da za a yi amfani da su wajen rarraba ofisoshi a Hedikwatar NERC da ke Abuja.

Bayanin yadda za a kashe wadannan makudan kudade na cikin Kasafin 2021 na kudaden da za a kashe a hukumar.

Shugaban NERC John Momoh ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai kan sa gaban kwamitin Majalisar Tarayya mai kula da Harkokin Lantarki da Makamashi domin kare kasafin NERC na 2021.

Momoh ya ce akwai bukatar zuba tebura da kujerun da kuma aikin rarraba wa ma’aikata ofis, a hedikwatar mai bene hawa takwas, wadda shekaru da dama bayan tarewa hedikwatar duk ba a zuba kayan ba.

Ya ce aiki na ci gaba da kankama, shi ya sa aka saka kudaden a cikin kasafin 2020 da 2021.

Momoh ya ce hukumar NERC ba ta iya kashe dukkan kudaden da aka ba ta a 2020 ba, saboda barkewar cutar korona.

Sai dai kuma an tambaye shi ya bayar da tantagaryar adadin kudaden da kujeru, twbura da kuma aikin karkasa ofis-ofis zai ci, sai Momoh ya Kasa.

Kwamiti ya nuna damuwa kan yadda hukuma za ta nemi kashe naira bilyan 2 wajen kayan kujeru da tebura, amma kuma ta kasa gabatar da kwangilar kuru-kuru.

Shugaban Kwamiti, Hon. Aliyu Magaji, ya yi barazanar goge kudaden kwangilar a cikin kasafin 2021.

“Ya za ka zo mana da bayanin aikin naira bilyan 2 a cikin rubutu layi daya? Idan ba ka shirya tsara yadda kwangilar ta ke dalla-dalla ba, to za mu cire ta daga kasafin 2021.” Inji shi.

Share.

game da Author