Hukumar SSS ta maida malamai 70 da sallama, bayan PREMIUM TIMES ta fallasa labarin

0

Hukumar Tsaro ta SSS ta maida malaman firamare da na sakandare su 70 da ta sallama daga aikin koyarwa a wata Community School, wadda mallakin SSS ce da ke Abuja.

An maida dukkan malaman kan aikin su ne bayan PREMIUM TIMES ta fallasa korar da aka yi masu a ranar 2 Ga Nuwamba, 2020.

Malaman dai an kore su ne bayan sun yi zanga-zangar lumana domin nuna damuwa da albashin su da ake yankewa, sai kuma korafin hukumar makarantar ta inganta matakan kula da su malaman.

Wasu malaman da wannan jarida ta zanta da su, sun ce, ko sun koma sai an zauna an tattauna batun albashin su da aka rika yanka, sake gindaya sabon albashin su da kuma inganta rayuwar su tukunna.

PREMIUM TIMES ta buga labarin an kori malaman firamare da na sakandare 71 a makarantar Hukumar SSS.

Sai dai kuma jin kadan bayan buga labarin, Hukumar SSS ta yi gaggawar maida su kan aikin su.

A labarin korar, an buga yadda aka kori akalla malaman firamare da na sakandare 71 ne aka yi wa korar-bazata a sakandaren Community Staff School, mallakar Jami’an SSS a Abuja.

Sallamar ta su ta biyo bayan kukan da su ka yi na neman inganta kula da su, wanda a lokacin da su ka fito nuna damuwar ta su, har tarwatsa su aka yi, ta hanyar dankara harbi a sama domin a razana su.

Takardar sallamar da aka raba wa kowane malamin mai dauke da ranar 2 Ga Nuwamba, ta fado kan teburin PREMIUM TIMES.

Da farko kafin a sallame su, an umarci iyayen dalibai cewa kowane yaro ya zauna a gida tsawon makonni biyu, domin a samu damar yi wa makarantar gyare-gyare.

Sai dai kuma abin da ya biyo bayan wannan, shi ne sanarwar sallamar dukkan malaman makarantar, na firamare daga hedimasta zuwa kowa da kowa.

An kuma koma bangaren sakandare aka sallami run aga firincifal har zuwa mai aiki dakin gwaji.

“Shugaban Hukumar SSS ya ba ni umarnin sanar da sallamar su daga aiki. Wannan ya faru ne saboda matsalar kuncin tattalin arziki da ya faru saboda korona.”

Sanarwar ta umarci duk mai wani abu mallakin makarantar, ya gaggauta damkawa ga hukumar makarantar.

Malaman sun dade su na kokawa kan rashin kula. Sannan su kuma iyayen yara sun koka saboda duk da halin da ake ciki, an yi karin kudin makaranta daga naira 70,000 zuwa naira 90,000.

Su kuma malamai sun ce an zaftare masu albashi da wasu hakkokin da su ka nema aka yi masu.

Share.

game da Author