Gidauniyar Tallafi ta TY Danjuma, mai suna VSF ta bayyana raba kayayyakin abinci da kariyar kamuwa daga korona har na naira bilyan 1 a wasu jihohin Arewa.
Za a fara raba kayayyakin a Gundumar Babban Birnin Tarayya, Abuja (FCT), Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Neja, Benuwai da kuma Filato.
VSF Gidauniya ce mai taimaka wa marasa galihu, wadda tsohon Hafsan Sojojin Najeriya, TY Danjuma ke shugabanta.
A cikin watan Afrilu Danjuma ya kafa kwamitin da zai yi aikin raba kayayyakin agaji a sansanonin masu gudun hijira a Arewacin kasar nan.
A ranar Laraba ce Shugaban Kwamitin Rabon Kayan Toyosi Ogunsiji ta raba wasu kayan ga Kungiyar Matan Najeriya (NCWS).
Ogunsiji ta ce wannan ne karo na uku an raba kayayyakin.
Da ta ke zantawa da PREMIUM TIMES, Ogunsiji ta ce farkon barkewar korona, Gidauniyar VSF ta raba kayan tallafi na kimanin naira bilyan biyu a jihohi 12 na kasar nan, cikin watannin Afrilu da Yuni.
Cikin wadanda Gidauniyar VSF ta raba wa kayayyaki a ranar Laraba har da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Kasa.
Kakakin Kwamitin Rabon Kayan Tallafin, Alkasim Abdulkadir, ya ce za a raba kayan abinci da su ka hada da shinkafa, man girki, kayan miya, wake, gishiri, masara da kayan kariya daga cutar korona ga gidaje 40,886 yayin da akalla mutum 204,330 ne za su ci gajiyar kai-tsaye.
Ya ce kashi 50 bisa 100 na kayayyakin za a bayar ga gwamnonin jihohin da za su moriyar su raba wa jama’a. Kashi 50 bisa 100 kuma kungiyoyi ne za a bai wa su raba.
Discussion about this post